✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Burina in kawo sauyi ga al’umma ta hanyar fim – A’isha Umar

Ai’sha Umar Muhammad sabuwar jaruma ce da ta shigo masana’antar fina-finan Hausa da kafar dama. Duk da cewa ba ta dade da shiga harkar fim…

Ai’sha Umar Muhammad sabuwar jaruma ce da ta shigo masana’antar fina-finan Hausa da kafar dama. Duk da cewa ba ta dade da shiga harkar fim ba, amma ta fito a manyan fina-finai. A hirarta da Aminiya ta bayyana dalilin da ya sa ta shiga harkar fim, burinta a harkar, ta kuma yi bayanin yadda take hada karatu da harkar fim; inda a yanzu take aji na hudu a Jami’ar Fasaha da Kimiyya ta Jihar Kano da ke Wudil. Ga yadda tattaunawar ta kasance:

Za mu fara da gabatarwa, shin wace ce A’isha Umar?
Assalamu alaikum, sunana A’isha Umar Muhammad. Ni mutum ce mai sauki kai da haba-haba da kuma wasa da dariya. An haife ni a Kano a shekarar 1982. Na yi makarantar firamare da sakandare da kuma ta gaba da sakandare a Kano, don haka zan iya cewa ni cikakkiyar ’yar Kano ce, duk da cewa mahaifina daga Jihar Adamawa yake, amma mahaifiyata ’yar Kano ce. Ni jaruma ce a masana’antar shirya fina-finan Hausa da aka fi sani da Kannywood. Na fito a fina-finai kamar shida, kasa da shekara daya da na fara harkar fim. A yanzu ina aji na hudu a Jami’ar Kimiyya da Fasaha ta Jihar Kano da ke Wudil, ina karanta kwas din Chemistry ne.
Ga shi kina karantar kwas din Chemistry, to me ya ja hankalinki kika shiga harkar fim?
Maganar gaskiya ita ce, sha’awa ce ta sanya na shiga harkar fim, domin tun ina karama nake da sha’awar harkar, ina sha’awar in rika kallon mutane a talabijin. Don haka zan iya cewa na dade da burin zama jaruma, kodayake a lokacin idan ka tambaye ni wacce hanya zan bi don in zama jaruma zan ce maka ban sani ba. Domin zan iya cewa a lokacin irin burace-burace ne na yara, amma abin kamar wasa sai ya zama da gaske, domin ina girma ina kara sha’awar zama jaruma, burin ya ki tafiya, sai karuwa yake yi, don haka a lokacin da na samu damar shiga harkar sai ban yi wata-wata ba, na rungume ta hannu bibbiyu.
Yaya iyayenki suka ji a lokacin da kika sanar da su za ki shiga harkar fim?
Sun san ’yarsu, sun kuma san abin da za ta iya, don haka ban sha wahala wajen shawo kansu ba, zan iya cewa ba su nuna tirjiya ba. A lokacin da na sanar da su zan fara harkar fim sai suka nuna damuwarsu dangane da makomar karatuna, domin suna ganin kamar harkar za ta kawo mini nakasu a bangaren karatuna. Ko kuma idan na ga harkar ta yi kyau sai in jefar da karatuna. Hakan ya sa na yi musu bayanin cewa ai karatuna yana sama da komai, domin duk abin da mutum zai yi sai yana da ilimi, don haka su kwantar da hankalinsu zan mayar da hankali a kan karatuna, da suka ji haka sai suka sa mini albarka, inda a yanzu ga shi na taka babban mataki a harkar, kuma bai kawo mini cikas a bangaren karatuna ba.
Yaya kike hada harkar fim da karatu kuma?
Na tsara lokacina yadda daya bangaren ba zai shafi daya ba. Idan lokacin karatu ya yi zafi sai in ajiye harkar fim, don in mayar da hankalina kan karatu, idan kuma abubuwa suka sassauta, sai in hada karatun da kuma harkar fim. Duk da yadda nake son fitowa a fina-finai amma ban yarda ya kawo mini cikas a bangaren karatuna ba.
Wane yanayi kika samu kanki a ciki lokacin da aka fara dora miki kyamara lokacin daukar fim dinki na farko?
Magana ta gaskiya na ji wani iri, inda na rika dari-dari, wani lokacin na rika jin faduwar gaba, na rika addu’ar Allah Ya taimake ni in cin ma burina, domin ba na so in yi abin kunya, wato in kasa yin abin da aka umarci in yi. Daga farko na kasa, amma yadda darakta ya rika yi mini magana cikin ruwan sanyi, da kuma kalmomi masu karfafa gwiwa sai na samu karfin gwiwar yin abin da ake so. Tun bayan dari-dari da fargabar da na yi a farko daga nan sai na goge, inda a yanzu na san ciki da wajen bangaren aktin.
Ko kin fito a matsayin babbar jaruma tun da kika fara fitowa a fim?
Daga yadda mutane suka rika fada mini ne ya tabbatar mini da cewa na shigo harkar da kafar dama, kasancewar idan ka duba kasa da shekara daya da fara harkar na fito a fina-finai da suka da da ‘Mijin Aro’ da ‘Mashi’ da ‘Bakin Alkalami’ da ‘Zullumi’ da kuma ‘Ta Faru Ta kare’ da sauransu. A cikin wadannan fina-finai na fito a matsayin babbar jaruma a fim din ‘Mashi’ da kuma ‘Zullumi.’ Haka ya nuna mini za a dama sosai da ni a Kannywood. Kuma ina gode wa Allah (SWT) da Ya ba ni wannan damar.
A matsayinki ta jaruma, wane buri kike so ki cin ma wa a Kannywood?
Babban burina shi ne in zama shahararriyar jaruma a duniya, inda lungu da sako za a rika maganata. A farko burina in zama jaruma, amma a yanzu kuma in zama shahararriyar jaruma a duniya. A yanzu zan iya cewa na yi amfani da aktin wajen yada al’adata a matsayina ta kabilar Hausa/Fulani da kuma ta Musulma. Aktin wani aiki ne na kawo sauyi a cikin al’umma, kuma na sha alwashin yin amfani da aktin wajen kawo sauyi a zukatan al’umma.
Idan dama ta samu, shin za ki iya fitowa a fina-finan Turanci na Nollywood?
Eh mana, me zai hana, matukar rol din da za a ba ni bai ci karo da al’adata da kuma addinina ba. Ina so a fahimci akwai abubuwa masu kyau da marasa kyau a duk sana’ar da mutum yake yi, ya rage mutum ya dauki wanda yake ga ya fiye masa ne. Akwai abubuwan da kowa ya sa a gaba, wanda yake karewa, don haka zan yi kokari wajen ganin na zama jakadar da za ta tallata al’adata da kuma yin nasiha ta hanyar addinina.
Yaya batun soyayya fa?
Ba ni da kowa.
Babu batun aure ke nan?
Tabbas zan yi aure, amma sai lokaci ya yi, amma dai kullum addu’ata ita ce in samu miji nagari wanda zai kasance mai kyakkyawar fahimta, mai tsoron Allah da kuma aiki tukuru, sannan ina so a sani daga na yi aure zan bar fitowa a fim kuma.
Mene ne sakonki ga masoyanki?
Ina so su ci gaba da yi mana addu’ar kariya daga makiya, sannan ina gode musu bisa ga soyayyar da suke nuna mini. Ina sanar da su zan ci gaba da faranta musu ta hanyar taka muhimmiyar rawa a fina-finan da zan rika fitowa.