Tarihinta:
Na yi karatun firamare a Sakkwato daga nan na wuce Kwalejin ’yan mata (GGC Sokoto), bayan na kammala na tafi Jami’ar Barna da na kare sai na wuce Ingila inda na yi karatu a jami’o’i daban daban na yi karatun digirina na biyu da kuma wasu kwasa- kwassai.
Na samu takardun yabo a wurare daban-daban a Amurka da Najeriya. Ina cikin kungiyoyin mata da na likitoci na kasa irin su (Women Federation of Nigeria) da (Medical Association of Nigeria) da sauransu. Yanzu kuma ni ce Mai bai wa Gwamnan Sakkwato Aminu Waziri Tambuwal shawara kan hakkin dan Adam da kungiyoyin sa kai a Sakkwato (NGO’s and Human Rights).
Nasarorin da ta samu:
Na samu nasarori da dama a rayuwata na yi karatuna cikin gata da kulawar iyaye don tun da nake ban taba cin karo da wani abu da ya zama matsala kai na ba. Bayan lambobin yabo da na samu a kasar nan da wajenta mafi girmamawa da na samu a 2013 da na ji dadinta shi ne na daliba mafi kwazo a Najeriya wacce tsohon Shugaban kasa Goodluck Jonathan ya ba ni. Haka kuma na ji dadi game da sarautar Garkuwar Wamba a Abuja da wadanda aka ba ni a Sakkwato.
kalubalen da ta fuskanta:
Halin rayuwa na fadi- tashi dole ka hadu da kalubale amma na gode Allah, haka nake ta fadi tashi in ga na taimaki talakawa da al’ummar Sakkwato. Kamar yadda ka sani aikina na taimako ne wajen kare hakkin dan Adam dole a hadu da abubuwan turjiya, Allah Ya taimakeni Na gode maSa.
Burinta a rayuwa:
Taimakon talaka ya samu nasara, ya ji dadi ya amfana. Sannan ‘ya’ya mata in taimaka wa karatunsu shi ne burina. Sannan ina sha’awar taimakon mata masu karatu a jami’o’i da manyan makarantu na gaba da sakandare, don kowace al’umma da zarar matansu sun samu ilimi to za a samu ci gaba mai ma’ana. Sannan ina da burin in ga ina kare hakkin dan Adam musamman marasa gata.
Abin da take son a tunata da shi:
Ina son na bar tarihi mai kyau (legacy) bayan na mutu a rika tunawa da alherina, a rika fadin Allah Sarki Hafsatu ita ce ta yi kaza da kaza, Jikanyar Doshiro ta gaji Sardauna da sauran magabata, Allah Ya ba ni iko.
Burinta na kuruciya ya cika:
Na cika buri, na nayi aure, ba wani buri a wurin mace kamar ta samu miji mai mutunci da kamala da daraja to ni na samu. Ni mata ce a wurin Honarabul Bala Kokani, ina zaman lafiya da tare da mijina muna mutunta juna.
Me za ki ce game da mukamin da kike kai a halin yanzu a matsayinki na mace:
Ina da kalubale masu yawa. A ofis di na na kawo tutocin kasashen duniya amma mutane ba su fahimce ni b,a aka rika surutu. Dalilina na yin haka shi ne duk kasar da ta ga muna tare da ita za ta rika tallafawa jihar Sakkawato da hakan zai samu mu samu ci gaba. Ina son in kawo canje canje masu ma’ana a kan haka nake kokarin tallafawa gwamnatin Sakkwato karkashin jagorancin Gwamna Aminu Waziri Tambuwal. Gaskiya yakamata Sakkwatawa su godewa gwamna, don mutum ne mai sanin yakamata da kuma hangen nesa yakamata mu taimake shi da fito da wasu hanyoyi da za mu kara taimakon jihar mu, kan haka ne nake son a kara hakuri da ‘yar Galadima. Harkokin aiki akwai wahala sai da na shigo ne na kara tabbatar da gwamna Tambuwal da Sanata Wanakko suna kokari sosai da jama’a. Ba na hutu koyaushe za ka ji an kira ni karfe biyu na dare kan kes na hakkin dan Adam, ashe haka shugabanci yake? Mu yi wa shugabanninmu addu’a.
Kina shiga har kauyuka a yayin da kike gudanar da aiki?
Albishirinka, yanzu haka na tsara yin yekuwa ta wayar da kai a kananan hukumomi 23. Zan zauna da Kwamishinan kananan hukumomi don tsara yadda ayyukkan ofishina za su amfani mutanen karkara bayan na biranen, kuma malaman addini ma za mu shigo da su don aikin da muke yi addini ya yarda mutane su san hakkinsu, duk wanda ba ya da karfi wajen kwatar hakkinsa sai hukuma ta shiga ciki don a amso masa. Akwai bukatar yin wa’azi na sanin hakkin Allah. Da iyaye da matan aure da mazaje da yara gaba daya mata su sani Allah ya amince a yi mata hudu su ko maza su sani su ba mata hakkinsu. Ofishina ya yi ta gyara aure da kwato hakkin al’umma a kotu da bai wa mata shawara su daina walakanta miji. In ba girmamawa to ba kyautatawa, Allah ne Ya ce a yi aure, malamai su kara dage damtse don matsala ta yi yawa a kotu da ofishina.
Zuwan yara mata makaranta:
Na gamsu, yanzu a Sakkwato mata suna zuwa makaranta fiye da in da aka fito. Gwargwado ana neman ilmi, an san amfaninsa da ci gabansa sai dai akwai bukatar iyaye su kara kulawa, duk da ana samun sauyin da ake bukata.
Shawarar ta ga mata:
Mata na kokari sosai wajen kare mutuncinsu, saura da me? su kara tashi tsaye su nemawa kansu ta hanyar da addini da al’ada suka gamsu da ita. Sabon Allah ba ya kawo masu mafita, duk wacce ta ji tsoron Allah, ta tsaya a matsayinta za ta samu gudunmuwa daga gareSa a cikin sauki. Mata mu rike Allah don Shi ne abin riko, Majinginar marasa galihu da wadanda aka dauka ba kowa ba.