Hajiya Dijatu Yerima Balla mace ce mai kwazo da hazaka a wajen tafiyartar da rayuwar yau da kullum. Haifaffiyar karamar hukumar Gombi ce a Jihar Adamawa. Sannan ita ce Shugaban makarantar Nadi. A wannan zantawar da ta yi da wakiliyar Zinariya, ta fadi irin kalubalen da ta fuskanta a lokacin da take kokarin kafa makarantarta.
Tarihinta:
Sunana Dijatu Yerima Balla. An haife ni a ranar 30 ga watan Augusta, 1959 a karamar Hukumar Gombi na Jihar Adamawa. Na yi karatun firamare a Gombi har zuwa aji biyu, a lokacin an yi Jihohin Arewa maso Gabas, daga nan sai aiki ya kai mahaifina Maiduguri sai muka koma can. Daga nan sai na cigaba da karatun firamare a Shehu Garbai a Borno. Shegaban makarantarmu Baturiya ce. Mun samu ilimi mai inganci wanda babu ha’inci a ciki ko kadan, domin a lokacin ana karantar da mu sosai sannan ana ba mu lafiyayyen abinci a makarantar kamar tsire da lemu da sauransu. Komai na makarantar a lokacin ana yin sa ne a bisa tsarin turawa. A lokacin mahaifina ya kasance Kwamishina sai ana zuwa daukarmu da motar Land Rober.
Daga nan sai na yi karatun Sakandare a Kwalejin gwamnati ta ’yan mata da ke Maiduguri (G.G.S.S) da na gama sai na tafi Kwalejin Horar da Malamai ta Bauchi (Bauchi Teacher’s College) sai na shiga fanin ilimi a gredi na biyu da niyyar idan na gama karatun sai na yi aure.
Da na yi aure sai na tafi Amurka inda na yi karatun Diploma a koyon dinki muna dawowa Najeriya a lokacin Jihar Gongola ta koma Jihar Adamawa. A shekarar 1976, sai na fara aikin koyarwa da shaidar karatu ta Grade I inda na kanrantar a Kwalejin ’yan mata, GGSS Yola. Na yi aiki har zuwa shekarar 1981, sannan na koma kara karatu a Jami’ar Maiduguri inda na karanci fannin ilimi da koyon harshen Turanci sannan na kammala a shekarar 1985.
Yadda na kafa makarantar Nadi:
Da na gama a shekarar 1985, sai na je bautar kasa na dawo. A lokacin ina Sakandare akwai wata malamata tana koyar da mu tarihi ina sonta sosai tun a lokacin na yi sha’awar zama malamar makaranta kuma na yi sha’awar bude makaranta. Da na dawo aiki sai na yanke shawarar bude makaranta domin a lokacin babu makarantu da yawa. Akwai wata kawata Asma’u tana da yara biyu sai na ce ta ba ni ’yarta daya wacce ba ta fara makaranta ba sai na bude makarantar da ita sunanta A’isha. Akwai wani yayana wanda ya ba ni gida da na fada masa manufata na bude makaranta. Sannan akwai wata ’yar Ghana wacce na yi wa magana ta taimakamin wajen bude makarantar sai ta zo muka fara, ita ma ta kawo nata ’yar. Da yara biyu na bude makarantana a shekarar 1988. A cikin wannan shekarar ce nake sa ran makarantar za cika shekara talatin. Makarantar ta samo suna NADI ne daga sunan ’yar’uwata Nafisa da ni Dijatu idan ka hada sunan za ka samu NADI.
Wanda na fi shakuwa a tsakanin iyayena:
Na fi shakuwa da mahaifina. Mahaifina mutum ne mai magana daya. Idan ya fadi abu ba ya canzawa. Ga tsayawa a kan gaskiya. ba ya bambanta tsakanin ’ya’yansa mata da maza. Ya sanya mu makaranta gaba dayanmu sannan babbar yayarmu ita ce likita mace ta farko a yankin Arewacin Najeriya. In dai za ka yi karatu to mahaifina zai kai ka ko’ina. Aiki da fadin gaskiya na daya daga cikin halayyar mahaifina da na gada.
Yadda na hadu da maigidana:
Mun hadu da shi ne a Maiduguri a lokacin na kammala karatun sakandarena sai muka yi aure a shekarar 1975. Sannan Allah Ya albarkace mu da da a shekarar 1979. Kuma shi ne kadai dan da na mallaka kawo yanzu. Yanzu dai ina da jikoki uku.
Abin da ba zan taba mantawa da shi ba a lokacin da nake karama:
A lokacin mun yi jarabawa sai ba mu ci ba. A lokacin ina da wani yayana wanda ya dawo daga Rasha kuma ya yi karatun Dokha (Phd) a fanin lissafi. Sai aka rufe mu a daki shi yayan namu zai ba mu aiki sai mu yi idan bamu ci ba ya sake ba mu wani sai da muka gane. Ba zan taba mantawa da wannan ba.
Sirrin zaman aure:
A kasance masu yin gaskiya tsakanin ma’aurata da kuma yawan zaman yin sulhu da kin barin magana a ciki na daya daga sirrikan zaman aure. Kar mutum ya yi fushi ba tare da yin magana da mijinsa ko matarsa idan an yi magana a nan ne ake samo sulhu. Sannan a girmama juna.
Macen da take burgeni:
Ina son Oprah Winfred domin mace ce mai kwazo da kuma taimakawa al’umma. Duk wanda zai bar kasarsa sannan ya je wasu kasashe domin taimakon talakawa, mutum ne da yakamata a so. Ina son Hillary Clinton, tsohon shugaban Amurka Bill Clinton domin ba ta bari jita-jita ya raba ta da mijinta ba. Idan na ganta a yau zance mata tana burgeni.
Inda nafi sha’awar zuwa hutu:
A rayuwa ina sha’awar zuwa hutu domin tun da na fara aiki, nakan tara kudi a hankali domin yin tafiya a karshen shekara. Ina sha’awar zuwa Zimbabwe domin a lokacin da na je kasar a shekarar 1992, wajen ya yi min kyau sosai domin na ziyarci kogin Zanziba da sauransu.
Abincin da na fi sha’awa:
Ina son Tuwo da miyar kuka sannan teba da miyar dage-dage.
Burina a rayuwa:
AlhamdulillAh! Akwai abubuwa uku da nake son ganin na yi su. Da ma ina da burin gina makaranta, a wannan fanni burina ya cika sannan ina da burin bude wajen wasa da shakatawa ga manyan gobe, shi ma na cika wannan buri. Burina a yanzu shi ne na nemo tallafi ga masu kananan karfi a harkar lafiya da ganin cewa sun samu kyakyawar kulawa a asibitocin gwamnati. Misali idan aka je irin wadannan asibitocin sai a ga Nas tana kula da marasa lafiya masu yawa da suka fi karfinta kuma hakan bai dace ba. Yana da kyau a kara yawan ma’aikatan da ke kula da marasa lafiya a asibitoci don su rika bayar da cikakken kulawa ga marasa lafiya.
kalubalen da na fuskanta a rayuwa:
Gina makarantana na daya daga cikin babban kalubalen da na fuskanta a rayuwa. Domin a lokacin ba ni da isassun kudi sannan kawayena ba su ba ni karfin gwiwa ba. Sai dai na sanya wannan burin gina makaranta da kuma niyya. Sai kawayena su yi ta ce mini ba zan iya ba. Ko da na fara da yara biyun sai suka cigaba da ce min “wace irin makaranta
ce wannan mai dalibai biyu? amma duk da haka ban karaya ba. Sai da na yi shekara daya sannan yaran suka zama su shida. Da ba dan juriya da taimakon Allah ba a wannan lokacin da tuni na watsar da kafa tawa makarantar. Da na biye wa mutane, da ban tsinci kaina a wurin da nake a yanzu ba. Mutane ba za su taba ba ka kwarin gwiwa ba idan za ka yi abu mai kyau. A gaskiya a wannan lokacin na fuskanci babban kalubale.
Abin da nake so a tunani da shi:
Alhamdulillah! Ba gidan da na mallaka ba sannan ba kudin da nake da su a asusun ajiyar banki ba illa na zama mai farantawa yara rai domin yara biyun da na bude makarantar da su daya ya zama kwararren likita a kasar Ingilla sannan dayar kuma ta zama kwararriyar likita a kasar Ghana. Kuma akwai yara da dama wadanda suka cigaba a rayuwarsu. Ina son a tunani a matsayin macen da ta yi tsaye domin ganin yara sun sami ilimi mai amfani da albarka.
Shawara ga matasa:
Yana da kyau iyaye da manya su kasance masu bada shawarwari masu tasiri ga matasa, domin yawan yin magana wata rana yana sanya mutum canzawa zuwa hali mai kyau. A da mutum daya a anguwa zai iya yi wa yara da yawa fada kuma babu wanda zai ce uffam amma yanzu ko a makaranta daga an taba yaro sai a ga mahaifinsa ya rako shi washegari. Wannan ba taimakon yaro ake yi ba. Yana da kyau iyaye su farga da yi wa yaransu fada a duk lokacin da suka kauce hanya. boye laifukan danka ba kauna ba ce illa tabarbarewar tarbiyya.
Yakamata matasa su san cewa duk shawarar da aka ba su mai kyau su yi amfani da ita domin wata rana za su girbi ribarta. A koyi sana’a. Kwanciya tun safe har yamma ba abu mai kyau ba ne. Domin Allah Bai haliccemu domin mu zo duniya mu zauna ba.