Malama Halima Baba Ahmad mace ce mai mayar da hankali kan duk abin da ta sa a gaba musamman a fagen gyaran tarbiyyar matasa da fadakar da su da kuma yaki da cin hanci da rashawa. Hasali ma ita ce Shugabar wata kungiya mai zaman kanta mai suna Centre for Jubenile Delikuency Awareness a garin Bauchi. A zantawarta da wakilinmu ta tabo batutuwa da dama ciki har da tarihinta da nasarori da kuma irin kalubalen da ta fuskanta a rayuwa kamar haka:
Sunana da takaitaccen tarihin rayuwata
Sunana Halima Baba Ahmad. Ni haifaffiyar Bauchi ce, cikin karamar Hukumar Bauchi. Mahaifiyata kuma ta fito daga karamar Hukumar Darazo ne. Na yi makarantar firamare a kofar Fada, na yi sakandare a Kwalejin ’Yan mata da ke Bauchi. Na yi karatun sarrafa na’urar Kwamfuta, sannan na yi bincike a fannin gano matsalolin da suke addabar jama’a da hanyoyin da za a magance su musamman gurbacewar tarbiyyar matasa. Bayan na kammala sai na kafa wata cibiyar gyaran tarbiyyar matasa mai suna Center for Jubenile Delinkuency Awareness da nufin magance kangarewar yara da ake samu a yanzu da kuma fadakarwa kan yaki da cin hanci da rashawa. Alhamdulillahi tunda muka fara matasa da dama da al’ummarmu suna cin moriyar ayyukan wannan cibiya sannan muna hada kai da gwamnati da hukumomi domin samun nasarar wasu ayyukanmu.
Abin da ke janyo kangarewar yara a ganina
Dalilan suna da yawa daga mataki zuwa mataki na girman yaro. Ka san idan an haifi yaro akwai abubuwan da yake cin karo da su na kalubale. Sannan a kowane mataki irin tarabiyyar da iyaye suke ba shi da ita zai tashi don shi za ta yi masa jagora wajen tafiyar da rayuwarsa. Misali a lokacin da yake rarrafe zai iya cutar da kansa bai sani ba, sai in iyaye suna kula da shi har ya kai matakin iya tsayawa da kafafunsa har ya kai matakin da za a sanya shi a makaranta a lokacin shi kuma wasa ya fi so. Ka ga wannan mataki shi ake kira Adolescent inji malaman ilimin sanin halin dan Adam wato lokacin da bai kai shekara 20 ba a nan yake gwagwarmayar rayuwa. Domin ga gagara, ga tashen balaga ga makaranta kuma an fi bukatar ya yi karatu a lokacin don ya dauko hanyar girma. A nan ka ga ya shiga duniya don a gidansu yawansu bai kai na makaranta ba, yanzu ya shiga makaranta ya hadu da jama’a masu tarbiyya mabambanta kowa gidansu daban da irin tarbiyyarsu. A nan ne wani yaron zai hadu da abokan da za su iya sauya masa tarbiyya in iyaye da malamai ba su kula sosai ba. A nan ne kuma ya fi sha’awar wasa in ba a lura sosai ba wani abu na iya bijirowa ya dauke hankalinsa a karatu da kuma tarbiyyar da ya taso da ita ta gurbace. Wadansu kuma iyayen ba sa sanya ’ya’yansu a makaranta ka ga idan ya tashi ba ilimin addini ba na boko kuma in ya hadu da gurbatattun yara to abin yakan yi muni wanda in ba a yi sa’a ba lalacewarsa sai ta fi ta wadanda suka koya masa tun farko. Ka ga wadansu iyayen kuma ba sa bai wa yaron tarbiyya, idan iyaye suka kawar da ido a kan tarbiyyar yaro sai ka ga matsalar ta yi girma, in yaran suka hadu da mutane marasa kishi ko ’yan siyasa da ba su da kirki sai su yi amfani da su ta muguwar hanya.
Nasarorin da muka samu kawo yanzu
Alhamdulillahi mun samu nasarori da dama saboda yadda muke iya janyo su kangararrun yaran a jiki mu fadakar da su mu mayar da su makaranta. Wannan ya sa na samu nasarori masu yawa domin dubban yara sun koma makaranta, wadansu sun yi jarrabawa sun ci suna jami’a, wadansu yaran da suka shiga sara-suka ko shaye-shaye tuni muka fadakar da su sun koma karatu.
Yadda nake ganin harkar ilimi a yau
Gaskiya matsalar talauci a yau ta gallabi wadanda suke gudanar da harkar ilimi. A baya an fara samun sauki amma yanzu matsalar kudi ta sa wadanda ke zuwa makarantu masu zaman kansu ba sa iya zuwa domin ba za su iya biyan kudin makaranta ba. Yanzu haka akwai yaran da na sani suna so su yi jarrabawar gama sakandare amma ba su samu dama ba saboda ba kudi.
Burina a rayuwa
Burina a rayuwa in ga kangararrun yara suna gyara tarbiyya sun koma makaranta suna karatun boko da na addini. Kuma ina da burin in ga wannan aiki da nake yi na gyaran tarbiyya na samu nasara a kansa ya bunkasa ya mamaye kasa baki daya.
Abin da na fi sha’awa
Babu abin da na fi so kamar in ga an samu hanyar bai wa al’umma ilimi domin shi ne gishirin zaman duniya. Duk abin da za ka yi wa dan Adam don gina rayuwarsa a bayan ilimi yake, kuma ilimi na tafiya da tarbiyya ce idan har an samu ilimi koma zai biyo baya.
Abin da ya fi bata min rai
Rashin tarbiyya da rashin sanin me ya kamata mu yi don gina al’umma!
kasashen da na taba ziyarta
Eh, ni ban yi yawo sosai ba, amma ina yawan zuwa kasar Masar, ina kuma sha’awar kasar saboda tarbiyyarsu da iliminsu domin a kasar abincin talaka da na mai kudi daya ne, ba bambanci. Komai suke yi akwai kishin kasa da kuma tarbiyya.
Abin da ke kai ni Masar
Nakan je birnin Alkahira ne in yi kasuwanci kuma ka san ana cewa tafiya mabudin ilimi.
Abincin da na fi so
Na fi sha’awar abincinmu na gargajiya. Ina son tuwo da miyar kuka, kuma ikon Allah yawancin abincin zamani bai dame ni ba.
Irin tufafin da na fi so
Na fi son atamfa, kuma ba ni da kayan ado, duk kayan da na sa zan iya shiga ko’ina da su.
Iyali
Batun iyali na taba yin aure har na haifi ’ya’ya biyu kuma sun kasance Allah Ya jarrabe su da ciwon Sikila kuma dukansu biyu Allah Ya yi musu rasuwa, daya shekararta bakwai, daya kuma biyar. A yanzu dai fiye da shekara 10 ba ni da aure, sai dai wannan aiki na gyaran tarbiyyar kangararrun matasa da kuma yakar cin hanci da rashin tarbiyya shi ne aikin da na sa a gaba.