✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Burina in fadakar da jama’a ta hanyar waka – Abdulhamid Matazu

A ganawar Aminiya da fasihin marubucin wakokin Hausa, Abdulhamid Matazu, marubucin ya bayyana irin yadda ya dauki waka da muhimmanci, sannan ya zayyano irin alfanun…

A ganawar Aminiya da fasihin marubucin wakokin Hausa, Abdulhamid Matazu, marubucin ya bayyana irin yadda ya dauki waka da muhimmanci, sannan ya zayyano irin alfanun da take da shi wajen fadakarwa ga al’umma. Ga yadda ganawar ta kasance:

Ko za ka bayyana mana tarihinka a takaice?

Sunana Abdulhamid Muhammad Sani. Kakana Alaramma Malam Idris, ya kasance babban liman a Matazu. An haife ni a unguwar kofar Gabas, Matazu Jihar Katsina shekaru 33 da suka wuce. Na fara karatun allo wurin mahaifina, wanda shi ne ya gaji kakanmu.
An kai ni makarantar Matazu Model Primary School a 1989. Na yi shiga makarantar sakandare ta ATC Katsina amma aka dauke ni zuwa Bauchi domin karatun allo. Daga nan na yi ta tafiya garuruwa daban-daban domin ci gaba da neman ilimin addini; inda na zauna garin Soba a Jihar Kaduna da dandume da Maska a Jihar Katsina da Jos a Jihar Filato, daga bisani na kuma komawa Bauchi, na ci gaba da neman ilimi daga malamaina da kuma gudanar da sauran al’amuran rayuwa. A haka ne na shiga makarantar Bauchi Institute for Arabic and Islamic Studies. Ban dade da farawa ba na fara aiki da jaridar Attatbik.
Bayan na yi shekara uku da fara makaranta sai na yi aure, na ci gaba da karatun har na samu shaidar Grade II. Kafin kammala karatun har Allah Ya ba ni ’ya’ya uku, Muhammad, Abdulhadi da Fatimatu. Bayan rasuwar mahaifinmu, sai na koma gida Matazu, inda a yanzu haka nake aikin koyarwa a makarantar firamare mai zaman kanta, mai suna Alhaji Ibrahim Babangida.
Me ya ja hankalinka ka fara rubuta waka?
Malam Musa dan’azumi, Shugaban makarantar da na fara karantarwa a ciki, wani dattijo ne kuma tsohon malamin makaranta da ya taba rike babbar makarantar da ke garinmu kuma da yawan ’yan bokon garinmu, da ke ji da kansu shi malaminsu ne. Bayan aje aikinsa aka dauke shi kwangila a makarantar. Hakika wannan bawan Allah na ji dadin zama da shi ainun duk da ba mu jima ba. Shi na fara yi wa wakar ta’aziyya. Kamar wasa kuwa sai na samar da baiti 15 mai dango hudu. A cikinta nake ta’aziyya da ban hakuri a gare mu duka.
Matakin farko da na fara dauka shi ne, na fara koya wa daliban makarantarmu, inda suka fara isar da sakon ga sauran jama’ar yankin. Sai dai ta kara fita ne a lokacin da aka gayyace ni in rera ta ga daliban babban makarantar garin namu. An buga wakar a takarda, inda aka yi ta saye. Ni dai na san na buga kwafi kadan amma na rika jin labarin cewa wasu sun rika gurzawa suna sayarwa.
Me ya tsunduma ka ka ci gaba da rubuta wakoki ba kakkautawa?
Tasirin da wakar ta’aziyyata ta yi, ya sa wasu daga manyan gari wadanda ma da yawansu dalibansa ne, suka yi mani alkawarin daukar nauyin buga wakar kuma in ma rubuta littafi duk don a yada don ’yan baya. Amma sai ba su cika alkawarin ba, gaskiya ko daya wannan abin bai mani dadi ba, wannan ya sa na bazama, naki zama haka nan.
Wani hutu da aka yi mana sai na dauki alkalamina na rubuta waka har guda biyu ta: 1-Zumunci da 2-Ilimi. Daga nan kuma sai na fara shiga yanar gizo, inda na fara haduwa da masana da ma ’yan koyo irina. Irin haka ne na hadu da Hajiya Anti Sadiya Kaduna, wacce ta yi mani sanadin haduwa da Malam Nasir G. Ahmad ’Yan Awaki. Shi ya duba mani wakokin biyu, ya yaba da aikin da na yi. Na ci gaba da hulda da masana, inda na zama dan Makarantar Malam Bambadiya ta Farfesa Ibrahim Malumfashi, na kuma zama memba a kungiyar Marubuta Katsina da ta Duniyar Marubuta Kano. Kuma ni dai memba ne a Majalisar Burin Zuciya ta jaridar Leadership Hausa da Gizago Kulob ta jaridar Aminya da ma wasu kungiyoyin da nake hankoron shiga yanzu haka.
Ya zuwa yanzu wakoki nawa ka rubuta?
Ina da waka ta fi arba’in kawo yanzu kuma da wata da nake rubutawa yanzu haka. Ina sa ran ta zama wakata da ta fi dukkan wakokina yawa da kuma fa’ida. Ina sa ran ta zama daya daga wakokin da aka rubuta masu yawa a kasar Hausa gaba daya, da yardar Allah.
Ko ka fara rera wakokinka a gidajen rediyo?
Bayan wani taro da na halarta na Gizago a garin Dutsin-ma, na rera wata waka mai suna ‘Firgihi!’ Waka ce da na rubuta a kan halin da kasarmu ke ciki na taraddadi da tsoro. A ciki nake bayyana halin da muke ciki, musamman mu nan Arewa. Bayan na gama rerawa, an tashi a taron sai Dokta Aliyu Ibrahim kankara da wani dan jarida na Gidan Rediyon Katsina suka kira ni a gefe suke shaida mani cewa in shirya don su kai ni gidan rediyo. Bayan dan lokaci na je Gidan Rediyon Katsina, na hadu Kabir S/kuka, inda ya yi mani jagaba, ya hada ni da shugaban watsa shirye-shirye, Malam Kabir Sha’iskawa. Wannan ce ranar da na fara zuwa gidan rediyo, daga baya na je Gidan Rediyon Bauchi, aka dauki wakokina har guda shida. Na koma Katsina Radiyo bision FM da Federal FM Katsina. Na kuma je Rahama FM da Freedom Radio, duk a Kano. Yanzu kuma ina shirin tafiya Sakkwato da Zamfara da Kaduna da yardar Allah.
Ko an taba karrama ka saboda wadannan wakoki na fasaha?
Hadaddiyar kungiyar Marubutan Katsina ta taba ba ni takardar yabo a wani gagarumin biki da aka yi a Jami’ar Umaru Musa ’Yar’adua da ke Katsina. Haka nan kuma Duniyar Marubuta ma ta taba ba ni kyautar musamman.
Kawo yanzu kana da kundin wakokinka da ka wallafa (diwani)?
A yanzu haka ban kai ga hakan ba tukunna, sai dai kusan komai ya kammala na samar da kundin wakokin nawa, ko yanzu a shirye nake kan hakan. Abinda nake hankoro shi ne, samar da babban kundin rubutattar waka da zai zama abin nazarta ga masana, dalibai da masu sha’awa. To amma ina bin komai a hankali tukun, na riga na san gaggawa ba ta kunu.
Wane abu ka samu ko kuma kake kan samu sanadin wakar da kake rubutawa mai cike da fasaha?
Babban abin da nake cewa na samu kuma nake kan samu su ne: 1-Aaddu’o’in da nakan samu daga da yawan jama’a da suka ji ko karanta wakokina. 2-Sabo da jama’a manya da kanana kuma suna haba-haba da ni. 3-Rashin zaman banza gare ni, domin a da nakan zauna haka nan ba na komai lokaci mai tsawo amma yanzu da yawan lokaci tunani nake ko rubutu.
Mene ne burinka a gaba kan rubutun waka?
Samar da wata hamshakiya kuma mashahuriyar waka da nake rubutawa a yanzu haka, fatana ta zama wata waka da da ba irinta a da aka rubuta da harshen hausa a fadin duniya baki daya, ta fuskar yawa da kuma fa’ida in sha Allah. Bayan wannan kuma sauran wakokina da na rubuta kan maudu’ai daban-daban, burina su zama littafin nazarta a makarantu da jami’oi da yardar Allah.
Cikin magabatan mawakan fasaha da wa kake koyi kuma me ya sa?
Na farko marigayi Dokkta Aliyu Namangi Zariya, sai kuma marigayi Malam Abubakar Ladan Zariya (OFR). Na dauke su ne saboda wakokina a kan turbarsu nake. Misali, su ba su amfani da kayan kida kowane iri, to ni ma haka ne. Da yawan mutane kan nemi na saka kidan to amma ni in so samu ne na fi son a irin hanyarsu, duk da cewa wasu za su ga ban shiga zamani ba. To dama kuma ni ba don zamanin nake rubuta waka ba. Ni dai burina ko bayan raina a ce me na yi wa al’ummata na karuwa da za a rika tunawa da ni don a rika yi mani addu’a. Don haka da yawan wakokina in ka cire irin wadda na yi mai suna ‘Jaririya’ da nake gode wa Allah da samun yarinyata ta hudu mai suna Khadijat, to sauran wakokina duk a kan al’umma ne kafataninsu. Ba ina yi ba ne don kudi ko makamancin hakan.
Kana da wani abu da ka yi a kan wadannan da kake bin turbarsu a waka?
kwarai da gaske, kamar Malam Ladan Zariya tuni na yi waka ta ta’aziyyar rasuwarsa kuma tuni har na fara samun yabo kan waka, daga masu gani a Facebook da kuma ji a gidajen radiyo.
Kana da alaka da mawakan da ke raye yanzu?
kwarai da gaske, ka ga kamar dai Malam Nasir G. Ahmad, zan iya cewa shi ne malamina a rubutun waka, don shi ne ya duba man wakokina guda biyu kuma muna da kyakkyawar alaka da aminina Malam Hafiz Koza Adamu. Malam Umar S. Ahmad shi ma muna matukar amfana da juna. Sannan shahararren fasihi Alhaji Aminu Ala, shi aka ba kyautata ya damka mani a hannu da kungiyar Marubutan Katsina ta ba ni.
Kana da kiran da za ka yi ga hukumomi da sauran jama’a game da waka?
Kamar yadda kowa ya sani, ba wata gwamnati ko sarauta da za ta zama gagarabadau sai da mawaka. Ga karamin misali na gudumuwa da suka ba da a siyasar kwanan nan.
Saboda haka ya zama wajibi ga gwamnati ta samar da kulawa ta musamman ga mawaka, musamman ga irinmu da muka mai da alkalumman rubuta wakarmu kan wayar da kai. Ga jama’a kuma, kirana shi ne mu rika daraja lokaci, mu daina yin rauni ga duk abin da za mu aikata, mu daina yin zaman banza.