✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Burina in bude katafaren kamfanin sarrafa nama -Basiru Ado

Wani matashi mai sana’ar fawa mai suna Malam Basiru Ado ya ce babban burinsa a sana’arsa ta fawa shi ne ya bude babban kamfanin suyar…

Wani matashi mai sana’ar fawa mai suna Malam Basiru Ado ya ce babban burinsa a sana’arsa ta fawa shi ne ya bude babban kamfanin suyar nama iri-iri.
Malam Basiru, dan kimanin shekaru 30, dan asalin garin Falgore da ke Jihar Kano ya yi furucin haka ne yayin da yake tattaunawa da Aminiya a shagonsa da ke Legas.
Ya ce, “Gaskiya ina da babban buri a cikin wannan sana’a tawa. Burina kuwa shi ne ina so na bude babban kamfanin sarrafa nama, inda zan rika yin tsire da suya da dambun nama da kilishi da sauransu. Ya zamana duk irin naman da ka zo nema  ba za ka rasa ba”.
Ya ci gaba da cewa, “Na yi shekaru 15 ina wannan sana’a ta fawa, amma na fi yin tsire. Kuma ita wannan sana’a na taso na gani yayyena suna yi, sai ni ma na shiga na koya. Ni ba gada na yi ba, koyon ta na yi. Kuma gaskiya na sha wahala daban-daban, amma na rika hakuri, har Allah Ya taimake ni na koya”.
Ya bayyana cewa ya fara sana’ar ne daga Arewa, sai daga bisani ya koma Jihar Legas. Ya bayyana wa wakilinmu cewa ya samu nasarori da yawa, musamman ma da yake har akwai wadanda suke cin abinci a karkashinsa.
Malam Basiru, wanda ya ce, ba ya fuskantar kalubale da yawa, ya bayyana cewa kula da namansa da yake yi ne ya sa mutane suke son huldar cinikayya da shi. “Ka ga ni mutum ne mai kula da tsafta. Ba na son kazanta, komai nawa tsaf-tsaf za ka gan shi. Duk ina yin haka ne kuwa domin duk wanda ya ga namana, zai yi
marmarinsa ya saya. Kuma ina kyautata naman ta yadda zai kasance mai dadi kuma yana gasarwa ga duk wanda ya saye shi. Haka nan duk wata doka ta tsafta da kiyaye nama muna kokarin kiyaye ta”. Inji shi.