✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Burin sabuwar gasar rubutu ta bunkasa adabin Hausa – Farfesa Ibrahim Malumfashi

A kwanan nan ne Makarantar Malam Bambadiyya a karkashin jagorancin Farfesa Ibrahim Malumfashi da hadin gwiwar kamfanin Pleasant Library and Books karkashin shugabancin Dokta Muttaka…

A kwanan nan ne Makarantar Malam Bambadiyya a karkashin jagorancin Farfesa Ibrahim Malumfashi da hadin gwiwar kamfanin Pleasant Library and Books karkashin shugabancin Dokta Muttaka Rabe Darma, suka fito da Gasar Rubutun Gajerun Labarai ga marubutan Hausa na ko’ina a duniya. Aminiya ta tattauna da Farfesa Malumfashi, inda ya bayyana tarihin ire-iren gasar da aka taba gudanarwarwa a kasar Hausa da kuma cikakken bayani game da ita wannan sabuwar gasa da suka kirkiro. Ga yadda tattaunawar ta gudana:

 

Dangane da gasa a adabin Hausa, ko za ka yi mana tariyar tarihin ire-iren gasar rubutu da aka taba yi a Hausa, tun daga ta farko zuwa yau?

Gasa ta farko da aka gudanar a kasar Hausa ta wanzu ne a shekarar 1927, wadda aka gabatar a makarantar Midil da ke Katsina tsakanin daliban makarantar, wadda kuma Abubakar Kagara (wanda daga baya aka fi sani da Abubakar Imam) ya lashe gasar, aka ba shi tukwici na fam daya.

 

Wane littafi ke nan ya rubuta, ya sunansa, me kuma ya kunsa?

Abin takaici shi ne, littafin ba a buga shi ba. Shi kuma Abubakar Kagara da ya rubuta shi har ya ci gasar da aka tambaye shi ko zai iya tuna sunan littafi ko abin da ya kunsa, ya bayyana cewa, bai iya tunawa, domin an dade, kuma bai da kwafe. Ke nan in da an buga ko ajiye wannan littafi zuwa yau da shi ne za a ce littafin Hausa na farko na hikaya da wani ya rubuta a kasar Hausa.

 

Ita hukumar makarantar Midil ta Katsina wane tsari ta bi da yin hangen nesa domin gabatar da wannan gasa?

Duk da cewa hukumar makarantar ce ta tsara da shirya wannan gasa, amma tunanin yin haka ba daga wurin hukumar Makarantar ya samo asali ba. Tunani ne da Turawan mulkin mallaka suka zo da shi domin samar da rubutattun labarai na Hausa, musamman ganin cewa malaman addini da suka yi karatun boko da farko sun kyamaci shirga karya a cikin takarda. Saboda haka aka fito da gasa da bayar da kazar karfi don a ja ra’ayinsu. Tun da farko dai  an fara samar da gasa ne a lokacin da aka samar da Hukumar kasa Da kasa Ta Nazarin Harsuna da Al’adun Afirka wadda kungiyar Afrika da kuma Mujallar da take bugawa mai suna Afrika suke gabatarwa tun daga shekarar 1908. Abin lura shi ne ba a kasar Hausa aka fara gudanar da wannan tsari ba, domin wannnan hukuma ta shirya gasar rubutun labarai cikin harsunan Afirka da dama ne ana kuma buga rahotansu a cikin mujallar. Daga nan ne Turawa suka shiga kira ga sauran kasashen da ba su fara gasar ba da su yi azama kafin a kawo kan su. Wannan ne ya sa hukumar Makarantar Midil ta Katsina ta shirya waccan gasa ta 1927, tamkar zakaran-gwajin-dafi. Sai a shekarar 1929 wannan gasa ta Afirka ta iso ga Hausawa.

Su wa suka shiga wannan gasa ta Afirka daga kasar Hausa?

Yawancin wadanda suka shiga gasar ta 1929, malaman makarantun boko ne. Kuma kamar yadda na yi bayani, gasa ce ta Afirka, cikin harsuna daban-daban. A wannan gasa an karbi littattafai guda 37 ne daga masu sha’awa. Guda 10 a cikin harshen Hausa aka aiko da su, guda 15 kuma a cikin harshen Suto, sai guda 9  a cikin harshen Ganda da kuma guda 2 a cikin harshen Madingo, sai kwara daya a cikin harshen Mende.

Littafin wani da ake ce da shi Komane, mai taken  Esela e isang phethehong  a cikin harshen Suto da kuma na wani da ake ce da shi Lwanga, mai taken Ebyafayo bya Baganda a cikin harshen Ganda, su ne suka zo na biyu, ba wanda ya yi nasarar zama na daya, saura kuwa a cikin harsunan da suka rage, duk sun sami yabo ne kurum, amma ba su ci gasar ba.

 

Su wa aka yaba wa daga kasar Hausa a waccan lokaci?

Nazarin da aka yi ya nuna cewa littattafan da suka sha yabo daga harshen Hausa sun kasance kamar haka. Akwai littafin H.B.G. Nuhu, mai taken Hausa Stories da na  Malam Dodo shi ma Hausa Stories ya kira shi, sai na  Malam Ahemet Metteden, mai suna Zaman Dara da na Malam Bello Kagara mai taken Littafin Karatu Na Hausa, sai kuma na Malam Nagwamatse, mai suna Takobin Gaskiya.

Za mu iya cewa wadannan littattafai su ne na farko ke nan da aka gani a kasar Hausa?

 

Haka ne, amma ba daya da aka buga ko ya zo hannun al’umma a kasar Hausa. An dai yaba musu, an kuma nuna cewa za su iya zama gwanaye a wannan harka, kamar kuma yadda daga baya wasu daga cikin su suka zama gwanayen, wato irin su Abubakar Kagara da Bello Kagara. Saboda haka za a iya cewa gasar da aka yi a shekarar 1933 ce ta samar da littattafan farko da za mu iya cewa sun wataya tsakanin al’ummar Hausawa. Ita kuma gasa ce da Hukumar Fassara ta Arewacin Nijeriya ta tsara da gudanarwa. A wannan gasar kuma littafin Ruwan Bagaja na Malam Abubakar Kagara shi ya zo na daya, sai kuma Gandoki na Malam Bello Kagara ya zo na biyu. Littafin Shaihu Umar na Malam Abubakar Bauchi, ya zo na uku, sai kuma Idon Matambayi na Malam Muhammadu Gwarzo ya zo na hudu. Littafin da ya yi na biyar shi ne Jiki Magayi na hadin gwiwar East da Tafida. Duk da cewa wadannan su ne aka zaba a matsayin wadanda suka ci gasar, akwai wasu da suka gamsar a lokacin gasar, aka tsara su don bugawa, amma ba a sami damar buga su ba, su ne kuwa Boka Buwaye na Malam Nagwamatse da kuma Yarima Abba na Malam Jumare Zariya.

 

Bayan nan an ci gaba da gabatar da gasa irin wadancan da aka yi a baya?

Ganin irin muhimmanci da nasarar da aka samu bisa bin tafarkin gasa, a shekarar 1978, hukumar wallafa da buga littattafai (NNPC) da ke Zaria ta shirya gasa domin samar da sababbin abubuwan karantawa. Wannan gasa ita ta samar da littatafai irin su Mallakin Zuciyata na Sulaiman Ibrahim Katsina da kuma So Aljannar Duniya na Hafsat Abdulwaheed da kuma Amadi na Malam Amah na Magaji danbatta. Haka kuma a shekarar 1980 da hadin gwiwar Hukumar Al’adu ta kasa, Hukumar ta NNPC da ke Zariya sun sake aza wata gasar da ta samar da zakaru da littattafai irin su Turmin Danya na Sulaiman Ibrahim Katsina da karshen Alewa kasa na Bature Gagare da kuma Zabi Naka na Mannir Mamman da wasu da dama.

An kuma samu karin wata gasar ta samar da littattafai a shekarar 1994, wadda Hukumar Al’adu ta Jihar Kaduna ta shirya, ita ce kuma ta fito da marubuta irin su Mahmoud Barau Bambale da Ibrahim Sheme da Shafi’u Magaji Usman da wasu da dama. An kuma ci gaba da gabatar da gasa irin wannan daga shekarar 2007, lokacin da wata mata Hajiya Bilkisu karaye ta dauki nauyin gudanar da ita a madadin mijinta Injiniya Bashir karaye da ya rasu. An yi wannan gasa har zuwa shekarar 2009 ta kuma samar da littattafai da marubuta wadanda aka sani da wadanda a lokacin suka fara tashe.

Za mu kammala makon gobe