Mene ne takaitaccen tarihinki?
Sunana Hajiya Fati Ladan kuma ni haifaffiyar garin Kaduna ce, na yi karatuna tun daga firamare zuwa sakandare zuwa jami’a duk a Kaduna. Kuma kafin in fara jami’a, na fara harkar fim din Hausa. A shekarar 2013 bayan Allah Ya hada ni da mijina mun yi aure sai na ci gaba da karatuna.
A lokacin da tauraruwarki ke haskawa sai kwasam kika yi aure. Me ya ja ra’ayinki?
Ai burina ke nan. Tunda na shiga harkar wadanda suke tare da ni sun san cewa burina kullum shi ne da na fara tashe Allah Ya fitar min da miji in yi aure. Kusan zan ce addu’ata ce Allah Ya karba.
Wadansu na ganin idan ’yan fim suka yi aure zama na yi musu wahala amma ke sai ga shi kin zauna hankali kwance, mene ne sirrin?
Sirrin kawai shi ne hakuri.
Wane ne mijinki?
Yarima Shatima kuma shi mutum ne mai hakuri da son jama’a da kuma barkwanci da kuma nuna soyayya sosai. Kafin in aure shi sai da na san ko shi wane ne domin ya fada min tarihinsa, saboda haka ban yi auren da ka ba. Na san wa na aura.
Wadansu na cewa idan ’yar fim ta yi aure akan samu masu zuwa su zugata ta fita. Wace dabara kike yi amfani da ita wadda har yanzu kike zaune da mijinki lafiya?
Na yi katanga ce, ka san Hausawa na cewa sai bango ya tsage kadangare ke samun shiga. Gaskiya ni dabarar ita ce ban ba da kofa ga irin wadannan mutane su shigo min gida ba. Ina ganin wannan katanga da na yi da kuma taimakon Allah Ya sa nake samun nasara.
Idan kika ce katanga ke nan kin kaurace wa abokan da kika yi harkar fim da su?
Muna mu’amala da wadanda muka yi harkar fim tare da su kuma babu abin da ya canja . Da na ce katanga ba wai ina nufin ga ’yan fim kadai ba, ai su masu son hana ruwa gudu ai ba a cikin harkar fim kawai suke ba. A ko’ina za ka iya haduwa da su ko makwabta ko abokan zamanka. Idan ka ce ka yi katanga ba wai kana nufin mutanen da kuke sana’a tare da suke da matsala ba kadai. Idan ka yi katanga kana nufin ka killace kanka daga irin wadannan tsirarun mutane da ke nufin kawo maka matsala ko hana ruwa gudu a cikin zamantakewarka da mai gidanka.
Idan kika waiwaya kika ga yadda ake yin fim a yanzu da yadda kuka yi a zamaninki yaya kike ji?
Gaskiya akwai bambanci domin zan iya cewa kusan shekara biyar ke nan rabona da Industiri. Kuma ina zama ina dan kallo jifa-jifa ina kuma ganin yadda abubuwa suka canja ba kamar yadda muke namu ba.
Chanji wani iri?
Eh! To abubuwa dai sun canja misali kamar yadda ake shiryawa yanzu kusan an fi ba da karfi a kan soyyaya gaba daya. Idan kuma ka duba za ka ga akasari rawa da waka sun fi karfin sakon da ake son isarwa. Yanzu idan ka kalli fim sai ka ga rawa da waka sun cinye labarin fim din. Mu kuma a lokacinmu ba mu cika raye-raye haka ba.
Ko kina kewar Industiri?
A’a, ba na kewar Industiri gaskiya.
Yanzu wane abu da ke daukar hankali a kan ’yan fim shi ne yawan fadace-fadace a tsakaninsu wanda hakan ba a san shi sosai a zamaninki ba, me za ki ce?
Ko a lokacinmu ana fada amma ba yadda ake yi ba a yanzu. Wanda ake yi a yanzu ya bambata da irin na wancan lokaci. Saboda yanzu babu girmama na gaba, gaskiya kowa yanzu yana da damar yin abin da yake so. Sai ka ga yarinya ta shigo Youtube ko Instagram ta yi abin da take so. Wanda mu a wancan lokaci ba mu yin haka.
Yanzu karancin tarbiyya da girmama na gaba ya yi yawa sosai a Industiri. Kuma abin takaici yanzu shi ne ba babba ba yaro. Manyan ba su iya yi wa kanana fada domin su ma suna yi. Manyan ya kamata su rika hakuri da junansu saboda kanana su taso su koya.
Yanzu idan kika samu dama za ki iya shirya fim dinki?
Lokacin da na yi aure ina da wannan tunani, amma a yanzu da abubuwa suka yi min yawa ina kasuwancina tare da karatu tunanin hakan ya dan ragu ba kamar da ba. Amma ko a yanzu din idan da hali zan iya yi.
Idan kika zauna kina kallon fina-finanki yaya kike ji a ranki?
(Dariya). Babu komai kawai dai nakan ji dadi.
Ba a cika ganin Fati Ladan wajen bukukuwan ’yan fim ba me ya sa haka?
Ba wai don ban son mutane ba ne a’a, ina son mutane amma kuma ina ganin Allah Ya yi ni ban cika son shiga harkar biki ba. Ni ina ganin ko lokacin da na yi karatu kawayena uku ne kawai kuma ba wai don ban da son mutane ba ne. Sai dai kawai a lokacin Allah Ya yi ne mai gudun magana, shi ya sa wani lokaci nake kebance kaina don gudun abin da zai je ya dawo, shi ne kawai.
A yanzu yaya mu’amalarki take da iyayen gidanku na da a Industiri?
Muna ci gaba da mu’amala har bayan na yi aure kuma suna ci gaba da mu’amala da mai gidana. Suna kuma da kyakkyawar alaka da mai gidana. Mutunci ne da aka kulla kuma har yanzu ba a yanke ba.
Me za ki iya tunawa lokacin da kike fim wanda idan kika tuna sai ki rika dariya?
Abin da idan na tuna nake jin dadi shi ne lokacin da kowa ke gudun ya saka Fati Ladan a fim saboda wasu na ganin ina da matsala domin tsohon mijina ya zo ya min sharrin cewa ni matar aure ce, amma nake fim har ta kai kowa na guduna. Idan na zo wadansu har tashi suke yi. Ana cikin haka ne kurum sai Ali Nuhu ya zo ya saka ni a wani fim mai suna Adamsi. Shi ne kuma fim din da ya daga ni kuma shi ne fim din da aka san ni da shi. Shi ne kuma fim din da nake tinkaho da shi har yanzu.
Bayan aure sai ga shi Allah Ya azurta ki da haihuwa, yaya kika ji a ranki?
Na yi farin ciki sosai wanda ba zai misaltu ba, saboda dama burina ke nan. Babu buri ga ’ya mace da ya wuce ta yi aure ta zauna lafiya da mijinta sannan Allah Ya ba ta haihuwa. Saboda haka na yi farin ciki sosai domin idan ka duba cikin yardar Allah an samu jinkiri amma daga baya ya zama mana alheri. Tunda ga shi Allah Ya azurta mu da ’ya mace a yanzu.
Kasancewar an dan samu jinkiri wajen haihuwa, ko kin lura akwai damuwa tare da shi?
Gaskiya ban gani ba ko daya, domin kusan shi ne ma ke kwantar min da hankali. Yakan fada min cewa shi fa da da da babu da duk haka za mu zauna. Kuma a bangaren gidansu ma ban samu wata matsala ba saboda gidansu ba a taba nuna min wani bambaci ba. Yadda nake sakewa in yi wani abu a gidansu ba na ma iya yi a gidanmu.
Ko kin taba fuskantar wani kalubale da masoyanki kina tare da mijinki wadansu su nemi za su dauki hoto da ke?
A cikin garin nan ma na dan fuskanci irin wannan matsala musamman bayan mun yi aure. Za ka ga idan mun fito tare da shi sai ka ga an zo an ce wai za a yi hoto da ni. Wani lokaci yana zaune ma sai ka ga wani na neman ya tunkude min miji. Idan na ce zan yi fada sai ya ce a’a, ki yi hakuri masoyanki ne.
A karshe ko kina kira da ga masoyanki?
Godiya ce ta musamman a gare su kuma Allah Ya bar kauna kuma addu’arsu da suke mana muna ganin haske sosai a zamantakewarmu, saboda kusan shekararmu shida ke nan muna tare da shi amma cikin yardar Allah mun kawo wannan lokaci duk da ganin da wadansu ke yi ba za a zauna ba. Wadansu gani suke ma bayan wata uku da aure za a fita, ga shi Allah Ya kawo mu wannan lokaci. Wannan duk addu’ar masoya ce mun kuma gode musu sosai. Allah Ya kara so da kauna a tsakaninmu da su.