✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Bunkasar inshorar Takaful a Najeriya

Inshorar Takaful na bunkasa a Najeriya fiye da inshorar al’ada da aka saba da ita, a cewar Manajan Daraktan kamfanin inshora na Takaful, Mista Momodu…

Inshorar Takaful na bunkasa a Najeriya fiye da inshorar al’ada da aka saba da ita, a cewar Manajan Daraktan kamfanin inshora na Takaful, Mista Momodu Musa Joof, inda ya bayyana cewa ba da dadewa ba (inshorar Musulunci) tsarin ya samar da kudin shiga har Naira miliyan 100 cikin watannin hudu da suka gabata kuma ya ci gabata da bunkasa daga kasha 30 zuwa 40 cikin 100 a shekara, yayin da inshorar al’ada ke kan doron bunkasa da kashi 5 cikin 100.

Joof ya ce Takaful tsari ne na raba riba tsakanin kamfani da abokin hulda. Takaful tsari ne na inshorar Musulunci, inda masu zuba kudinsu a matattarar hada-hada don bai wa juna tabbacin karya lagon asara ko illa. Kamfanonin inshorar Takaful an bullo da su a matsayin wata dama ta daban a hada-hadar kasuwancin kamfanonin inshore, ba tare da ta’ammali da ruwa (riba) ba ko caca (al-maisir) da rashin tabbas (algharar) tsare-tsaren da shari’a ta haramta. Kamfanin inshora na Jaiz Takaful  da ke kan doron tsarin shari’a yanzy yana gudanar da hada-hadar kasuwancinsa ga Musulmi da wadanda ba Musulmi ba. Ya saba wa inshorar al’ada ta fuskar cewa Jaiz Takaful na karbar kudi daga abokin hulda na zubin inshorar. Idan ya yi asara kamfanin zai biya shi, idan kuwa bai yi ba za a raba ribar matattarar hada-hadar inshorar ga wadanda ba su yi asara a wannan shekarar ba.

Jaiz Takaful na daukar kaso 30 cikin 100 daga zubin kudin inshorar a matsayin ladar kula da ririta hada-hadar dukiya, kason da take amfani da shi wajen biyan albashin ma’aikata da masu hannun jari. Kashi 70 cikin 100 kuwa ana zuba wa ne a wani asusun ajiya na daban, wanda ake kira da asusun masu hada-hada. Ana amfani da kudin  ne wajen biyan ikirarin asara ko sake zubin inshorar ko kamasho ga masu shiga tsakani da masu sarrafa dukiya da wakilai da sauran kudin da doka ta kayyade. To ko mene ne ya ragu ana bin tsarin rabon kasawa a tsakanin wadanda ba su yi wata asara ba tsawon shekara. Takaful na kan doron ka’idar Musulunci ta Taawun ko taimakon hadin gwiwar juna. Zubin kudin da abokin hulda ya yi yana nan a matsayin jarinsa idan har bai yi asara ba.

Asalin Takaful ta fara ne a tsakanin kabilun Larabawan da ke da matattarar hada-hadar daukar nauyi, inda aka rika tursasa wadanda suka cutar da al’umma su biya diyya ga wata kabila  ko wanda suka citar ko magadansu.. daga bisani an fadada tsarin kan sauran hada-hadar rayuwa da ta hada da safarar teku (tafiyar jirgin ruwa), ta yadda idan masu hada-hada suka yi zubin kudin inshorar don bayar da kariya ga kowane mutum da ke cikin rukunin, wanda ya yi asarar a safarar jirgin ruwa.

Wadanda suka shiga tsarin takaful sun kulla dangantaka a tsakaninsu a matsayin masu hada-hada, wadanda suka amince da hadin gwiwa bayar da kariya ga asara ko illa da ta auku ga dayansu sai a fitar da kudi da aka asusun matatarar hada-hada. Mafi muhimmancin lamarin shi ne, a karshen shekarar kasuwanci, kowace riba aka ci a karkashin Takaful za a raba ta ne a tsakanin masu hada-hada da masu hannun jari bisa la’akari da kimar jarin da suka zuba. Wadanda suka shiga tsarin Takaful  za a raba riba da su kana bin da suka zuba bisa la’akari da hada-hadar kasuwancinsu na Takaful, wanda kamfanin inshorar Jaiz zai samar kan sharadin kimanta ribar da aka samu a karshen shekarar kasuwanci.

Jarin Takaful ana hada-hadar kasuwanci na halala da shi ne, wato kayayyakin da ba su da alaka da kudin ruwa. Irin wannanj jarin ba za a yi hada-hadar juya kudi da ruwa ba, sabpoda akwai bambanci tsakanin kudin ruwa da riba. Na biyu, wani kason kudin Takaful za a zuba shi a tsarin tabaru ko Sadaka, wanda tamkar biyan zakka ne.

Kariyar inshorar ana bayar da ita ne ga kowace hada-hada mai tsafta (da ba haramta ba) a karshen kowace shekjara, kuma ribar da kamfanin ya ci, kashi 80 cikin 100 za a rabata ne ga abokan hulda ko masu hada-hada wadanda ba su yi asara ba, har tsawon shekara. Wadanda kuwa suka yi asara suka ake fara biya kafin a raba riba. Kason da ake bai wa mabukata, wanda ake kira zakka shi ma ana fitar da shi ne kafin a raba riba.

Ganin yadda ’yan Najeriya ke kyarar kowane al’amari na inshore, muna da tabbacin cewa wannan nau’i ne mai kyau. Kuma dole ne shi ma a dora shi bisa doron tsattsauran tsarin lasisi da bibibiyar hada-hadar bisa klulawar Hukumar inshore ta kasa ta Najeriya (NAICOM) da aka dora wa alhakin kula da irin wannan masana’anta.