✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Buni ya yaba wa matasan Yobe kan watsi da zanga-zanga 

Kwanan nan mun ƙaddamar da gagarumin shirin ƙarfafa aikin noma da tabbatar da tsaro.

Gwamna Mai Mala Buni ya yaba wa al’ummar Jihar Yobe musamman matasa bisa yadda suka aminta da kiraye-kirayen da ake yi na ƙin amincewa da shiga zanga-zanga a daidai lokacin da jihar ke fita daga ƙalubalen tsaro da ta daɗe tana fuskanta.

Hakan na kunshe cikin wata sanarwa da babban daraktan yaɗa labarai na gwamnan, Mamman Muhammad ya raba wa manema labarai a birnin Damaturu.

Sanarwar ta ambato gwamnan na cewa,“Ina nuna farin cikina dangane da matakin da matasa suka dauka na janyewa daga zanga-zanga la’akari da halin da muka fito na rikicin masu tada ƙayar baya na tsawon lokaci.

“Al’ummar Yobe musamman ma matasanmu masu kishin ƙasa sun nuna ƙauna da kishin ƙasa ga jihar ta hanyar amsa kiraye-kirayen ƙin shiga zanga-zangar,” in ji shi.”

Gwamnan ya ba da tabbacin cewa gwamnatinsa za ta faɗaɗa manufofinta da shirye-shiryenta don bunƙasar tattalin arziki, da kuma tabbatar da ɗimbin masu cin moriyar shirye-shiryen sun yawaita.

“Kwanan nan mun ƙaddamar da gagarumin shirin ƙarfafa aikin noma domin bunƙasa shi don  tabbatar da wadatar abinci da tsaro a jihar.

“Kamar yadda kuka sani manoma 20 daga kowace mazaɓa cikin mazaɓu 178 da jihar ke da su suna cin moriyar shirin ƙarfafa aikin na gona, baya ga samar da ayyukan yi ga matasanmu da gwamnatin ke yi a dukkan sassan mazaɓun jihar.

Ya kuma ba da tabbacin cewa gwamnati za ta tabbatar da cewa Jihar Yobe ta zama abin koyi a fannin noman damina da na rani.

Gwamnan ya kuma ƙara ba da tabbacin cewa, da irin wannan fahimtar gwamnati za ta ci gaba da aiwatar da manufofi da tsare-tsare masu dacewa da jama’a don inganta rayuwar al’umma.