✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Buni Ya Rushe Majalisar Ciyamomin Yobe

Gwamna Mai Mala Buni na jihar Yobe ya amince da rusa dukkanin shugabannin Majalisun  kananan hukumomi 17 tare da kansilolinsu.

Gwamnan Yobe Mai Mala Buni ya sauke duk shugabannin majalisun  kananan hukumomi jihar tare da kansilolinsu.

Sanarwar na kunshe ne a cikin takardar sanarwar da Sakataren yada labarai na sakataren gwamnatin jihar, Malam Shuaibu Abdullahi, ya fitar a garin Damaturu.

Ya ce Gwamna Buni ya umarci dukkan shugabannin kananan hukumomin da su mika al’amuran kananan hukumominsu ga daraktocin gudanarwa na ma’aikata a ranar 25 ga watan Afrilu ko kuma kafin ranar.

A miniya ta ruwaito cewa Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Jihar Yobe (YSIEC) ta sanya ranar 25 ga watan Mayu domin gudanar da zaben kananan hukumomin.

Tun kafin lokacin ma ake samun rahoton cewar, sasu da ke da kudirin neman shugabancin kananan hukumomin ke kokarin kamun kafa a wurin masu ruwa tsakin gwamnatin don ganin hakar su ta cimmma ruwa.