Gwamna Mai Mala Buni na Jihar Yobe, ya janye dakatarwar da ya yi wa Shugaban Karamar Hukumar Machina, Honarabul Idrissa Alhaji Bukar Machina.
Ana iya tuna cewa dai a kwanakin baya ne aka dakatar da Idrissa Alhaji sakamakon zarginsa da rashin biyayya.
Sai dai a cikin wata takarda da ke dauke da sa hannun mai magana da yawun Sakataren Gwamnatin Yobe, Alhaji Shuaibu Abdullahi, ta ce an janye dakatarwar da aka yi wa Shugaban Karamar Hukumar ta Machina.
Sanarwar wacce aka raba wa manema labarai a Damaturu, ta ce an dage dakatarwar ne sakamakon bayyana nadamarsa da Idrissa Alhaji ya yi a rubuce cikin wasikar ba da hakuri.
Alhaji Abdullahi ya ce hakan ya nuna ba zai sake aikata abin da ake zargin sa da yi ba nan gaba wadda ya haifar da ta kai ga dakatar da shi da Gwamnan ya yi.
“Kafin sake mayar da shi kan kujerar jagorancin karamar hukumar sai da aka tattauna da ma’aikatan kananan hukumomin da kuma dukannin masu ruwa da tsaki domin ci gaban karamar hukumar Machina da jihar Yobe baki daya.”