Al’amura sun fara daidaita sakamakon sanya dokar taƙaita zirga-zirga a manyan garuruwan Potiskum, Gashu’a da Nguru, da Gwamnatin Yobe ta yi, bayan tarzomar da ta biyo bayan zanga-zangar tsadar rayuwa da aka fara a faɗin Najeriya, ranar 1 ga watan Augusta, 2024.
Gwamnatin jihar ta ɗauki matakin ne don daƙile ayyukan bara-gurbin da suka yi shigar burtu a zanga-zangar, wadda aka shirya ta lumana, suka riƙa ƙone-ƙone da wasoson dukiyar Jama’a.
An kafa dokar a garuruwan ne domin bai wa jami’an tsaro damar dawo da al’amurra yadda suke, da kuma katse hanzarin ɓata-gari daga wawushe kayan al’umma da makamantan su.
Jim kaɗan da ayyana dokar, aka sanu dawowar da doka da oda a faɗin jihar kuma zanga-zangar ta tsaya a faɗin jihar.
Har lokacin kammala wannan rahoton babu labarin ci gaba da gudanar da zanga-zangar a waɗannan garuruwa da ma faɗin jihar baki ɗaya.
A zantawarmu da wani magidanci Malam Mustapha Mai Kayan Miya da ke Gashuwa, ɗaya daga cikin garuruwan da aka saka dokar, ya bayyana cewa, “sa’o’i biyar da aka ba mu don gudanar da harkokin kasuwancinmu.
“Da zarar sun wuce za ka tarar da sauran cibiyoyin hada-hadar kasuwanci da gidajen mai da tasha sun ci gaba da kasancewa a kulle.”
Ya ƙara da cewa, “Yanzu haka zancen da muke da kai kasancewar lokacin fitarmu bai yi ba, kowa yana zaune a gida, kuma kawo yanzu babu wani yunƙurin wata zanga-zanga a nan garin na Gashuwa.”
Haka zancen yake a garin Nguru, inda wani ganau ya shaida mana cewa, jami’an tsaro suna ci gaba da sintiri da sanya ido don ganin ba a sake samun wata tarzoma ba.
Da yake tofa albarkacin bakinsa, Malam Alhaji Muhammad Kabiru daga Potiskum, ya bayyana cewar babu wani yunƙuri ko tashin hankali a garin.
Ya ce, “Face kawai jami’an tsaro suna ci gaba da zagaya lungu da saƙo domin ganin jama’a sun bi umurnin dokar takaita zirga-zirga da Gwamnatin jihar Yobe ta sanya.
“Ko shakka babu wannan dokar ta yi amfani sosai, saboda yadda ta dawo da al’amurra yadda suke yayin da jama’a ke ci gaba da gudanar da harkokinsu kamar kullum.
“Duk da yadda kasuwanni suka kasance a garƙame domin gudun kada ɓata-gari su fantsama cikin kasuwanni su aikata ɓarna, sai lokacin da kawai aka bayar don buɗe kasuwa wadda da zarar wa’adin da aka bayar don sake rufewa ya yi, sai kuma a sake garƙame ta.