✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Buni ya ba da umarnin sakin matashin da ya caccake shi

Gwamna Buni ya ce bai san da batun tsare matashin ba har sai da wani ya ja hankalinsa.

Gwamna Mai Mala Bunin na Jihar Yobe, ya ba da umarnin a gaggauta sakin matashin nan da aka tsare bisa zargin cin zarafinsa a shafin Facebook.

A ranar 11 ga Disamba jami’an tsaro suka cafke matashin a yankin Nguru inda aka dauke shi zuwa Sashen Binciken Manyan Laifuka na Rundunar ’Yan Sandan Jihar da ke Damaturu, babban birnin jihar.

A wata hira da Tashar Channels ta yi da mahaifin matashin Garba Isa, ya roki alfarmar a sako masa dansa.

Ya ce, “Na yi nadamar abin da dana ya aikata. Ni ba kowa ba ne, talaka ne mai wanki da guga, abin da dan nawa ya aikata bai yi daidai ba.

“Ina rokon Gwamna Mai Mala Buni da Rundunar ’Yan Sanda su yafe wa dana sannan su sake shi,” in ji Isa.

Sai dai kuma, sanarwar da ta fito ta hannun Darakta-Janar na Yada Labarai ga Ggwamnan, Mamman Mohammed, ranar Talata a Damaturu ta nuna Buni bai san da wannan batun ba.

Gwamnan ya ce ba daidai ba ne a tsare wani don ya ci zarafinsa ko ya caccake shi.

“Wannan shi ne tukwicin shugabanci, muna sane da haka, don haka ba zan ba da umarnin a kama ko tsare kowa kan haka ba.

“Ban san abin da ke faruwa ba har sai da wani ya ja hankalina, don haka na ba da umarni a gaggauta sakin shi,” in ji Buni kamar yadda sanarwar ta nuna.

Gwamnan ya ja hankalin jama’a kan a rika amfani da kafafen sada zumunta yadda ya kamata ta hanyar lura da ’yancin kowa.

(NAN)

%d bloggers like this: