✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Buni muka sani shugaban APC, ba kai ba —INEC ga Bello

INEC ta ce ita ba ta san Gwamnan Neja Abubakar Sani Bello a matsayin shugaban rikon jam'iyyar APC ba.

Hukumar Zabe ta Kasa (INEC) ta ce ba ta san Gwamnan Jihar Neja, Abubakar Sani Bello a matsayin shugaban jam’iyyar APC ba.

Hukumar ta aike da hakan ne a hukumance a amsarta ga Gwamna Abubakar Sani Bello, tana mai bayyana cewa ita Gwamnan Jihar Yobe, Mai Mala Buni, ta sani a matsayin shugaban rikon jam’iyyar.

“Tabbas APC ta aiko da wasika, INEC kuma ta ba da amsa saboda akwai batutuwa da suka shafi doka…Ba su yi abin da ya kamata ba,” inji wani babban jamim’in INEC.

Shi kuma wani jami’i hukumar ya ce ta tunasar da APC cewa Shugaban Jam’iyya ko Sakatarenta na kasa ne kadai ke da hurumin rubuta wa hukumar wasikar gayyata zuwa taron jam’iyyar.

Jami’an hukumar sun bukaci a sakaya sunansa saboda ba su da izinin yin magana a kan rikicin shugabancin da ya dababaiye APC a makon nan ba.

A ranar Laraba Gwamna Sani Bello ya aike wa INEC sako a matsayin Mukaddashin Shugaban APC na kasa, kuma shugaban kwamitin shirya babban taron jam’iyyar da take shirin gudanarwa a ranar 26 ga watan Maris da muke ciki.

A wasikar, gwamnan ya gayyaci INEC zuwa taron Kwamitin Zartarwar jam’iyyar na kasa, da za a gudanar a ranar Alhamis mai zuwa.

Amma  amsarta, INEC ta shaida mishi cewa ita Mai Mala Buni ta sani a matsayin Shugaban Rikon Jam’iyyar APC ba shi ba.

Karbe ragamar shugabanci

A ranar Litinin ne gwamnan na Jihar Neja ya karbe ragabar shugabancin jam’iyyar a hedikwatarta da ke Abuja, da ikirarin cewa ya samu amincewar Shugaban Kasa Muhammadu Buhari.

A cewarsa, Buhai ya ba da izinin cire Mai Mala Buni daga kujerar shugabancin jam’iyyar da kuma kwamitin babban taron jam’iyyar.

APC ta shiga rudani

Dambarwar dai ta haifar da rudani, musamman ganin yadda bayan wani taro a hedikwatar jam’iyyar, Gwamnan Jihar Neja, Abubakar Sani-Bello, ya bayyana kansa a matsayin shugaban rikon APC.

A ranar Laraba, Gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufai ya bayyana cewa an cire Buni ne da izinin Buhari.

El-Rufai ya zargi Buni, wanda ya je duba lafiyarsa a kasar waje, da haddasa rikice-rikicen da suka dabaibaye jam’iyyar, don haka aka maye gurbinsa da Gwamna Sani Bello, da amincewar gwamnonin 19 da jam’iyyar take da su.

Zuwa ranar Alhamis aka ga wata takarda da ba a tantance sahihancinta ba tana yawo cewa Buni ya mika ragamar shugabancin jam’iyyar ga Bello a matsayin riko, a tsawon lokacin da Bunin zai kasance ba ya Najeriya.

Sai dai kuma Gwamna Sani Bello ya ce bai san da wannna takardar ba.

‘INEC ba ta da masani’

Wasu majiyoyi da muka zanta da su sun bayyana cewa batun sauyin shugabancin APC na cike da rudani.

Wani jami’i hukumar da muka zanta da shi ya ce INEC ta tunasar da jam’iyyar cewa Shugaban Jam’iyya ko Sakatarenta na kasa ne kadai ke da hurumin rubuta wasikar gayyatar hukumar zuwa babban taron jam’iyyar.

A halin yanzu dai Sakatarern Kwamitin Babban Taron APC na kasa, Sanata John James Akpanudoedehe bai sai makomarsa ba a karkashin sabon shugabancin da Gwamna Bello ke irirari.

A takaice, a hukumance INEC ba ta san da zaman Gwamna Abubakar Sani Bello a matsayin shugaban rikon APC ba, ballanta ya samu hurumin aike mata da sako a hukumance.

Sashe na 82 (1) na Dokar Zabe ta 2022 ya wajabta wa kowace jam’iyyar siyasa mai rajista sanar da INEC kwana tun 21 kafin babban taronta na kasa, ko taron zaben shugabanninta ko na nada kwamitoci ko hadewa da wata jam’iyya ko zaben ’yan takara.

Sani Bello ya yi fatali da wasikar Buni

Aminiya ta ruwato El-Rufai yana cewa an sauke Buni ne, sabanin wasikar da ke yawo cewa ya mika wa Bello shugabancin kwamitin babban taron ja’iyyar ga Bello.

Bangaren Buni na ikirarin cewa tun kafin tafiyar Buni kasar waje domin duba lafiyarsa ya mika ragamar jam’iyyar a hukumance bisa tsari ga Gwamna Bello.

A wasikar da ke dauke da kwanan watan 28 ga Fabrairu, 2022, an ga cewa Buni na umartar Bello ya ci zama mukaddashin shugaban kwamitin taron na tsawon lokacin da Buni zai ga likita.

Wasikar da ake takaddama a kanta dai ta nuna tan tura kofin takardar ga INEC da  mambobin kwamitin taron.

Amma a ranar Alhamis, Bello ya shaida wa maneman labarai cewa kwamitin rikon jam’iyyar ba ta taba ganin wasikar da ake magana a kai ba.

An kuma tambaye shi game da gaskiyar nasa sabon sakataren jam’iyyar da zai maye gurbin Sanata John Jamesa Akpanudoedehe, gwamnan ya ce ba su yi wannan batu ba.

Maatakin gaggawa

Wani masanin shari’a da muka tattauna da shi a kan wannan dambarwa, ya bayyana martanin INEC ga jam’iyyar a matsayin “martanin da ba a taba ganin irinsa ba.”

Ya ce, “Jam’iyyar na kara jefa kanta a cikin tsaka-mai-wuya ta hanyar kumbiya-kumbiyar da take yi. Babu wata yanke da za a  iya bi a batun da ya shafi doka da shari’a.

“Idan har jam’iyya za ta sauya shugabancinta, dole ne a yi shi a hukumance kuma a fili INEC da jama’ar kasa su sani.

“Gaskiya ina ganin INEC taimaka musu ta yi da ta ja hankalinsu kan kuskuren da suke son su. Ya rage ruwansu, ko su gyara ko su ci gaba har matsalar ta rusa su a 2023,” inji shi.

Mun tsallake juyin mulkin farar hula —Akeredolu 

Gwamnan Jihar Ondo, Oluwarotimi Akeredolu, ya shaida wa magoya bayan jam’iyyar cewa ba su goyon bayan sauyin da aka samu a jam’iyyar, yana mai kira sabbin shugabannin da su tattara su tafi.

Akeredolu, a cikin wata sanarwa ya yi Buni ya yi kokarin bin zabin Buhari, yana mai cewa sun tsallake juyin mulkin farar hula da wasu masu neman mulki suka kirkira ta hanyar kafa shingen bogi.

APC za ta rushe idan ta kasa kafa kwamitin babban taro —Marafa

Sanata Kabiru Marafa, tsohon dan Majalisar Dattawa daga Jihar Zamfara, ya ce APC za ta rushe muddin ta kasa kafa kwamitin babban taron na ranar 26 ga watan Maris.

Sai dai kuma Marafa, ya bayyana cewa sunan kwamitin riko da shirya babban taron jam’iyyar haramtacce ne, ba ma maganar ya nada wani kwaitin ba.

Marafa ya yaba wa El-Rufai da wasu gwamnoni APC da ya ce sun yi abin da ya dace womin ceto jam’iyyar daga rudanin da ta fadi.

Sagir Kano Saleh, Ismail Mudashir, Abbas Jimoh & Idowu Isamotu