Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar Nasarawa Bola Longe, ya hana tayar da abubuwa masu kara yayin bukukuwan Kirsimeti da Sabuwar Shekara a Jihar.
Ya ba wa jami’an ’yan sanda da sauran hukumomin tsaro na jihar umarni da su sanya ido da kuma hana amfani da knockout.
- Mutum 300 sun kamu da COVID-19 a Nasarawa
- Hukuncin daurin rai-da-rai zai tabbata kan masu fyade a Nasarawa
- Wa ya babbake kaninsa kan satar N4,500 a jihar Nasarawa
- Wanda ake zargi da kashe Shugaban APC na Jihar Nasarawa ya shiga hannu
Ya kirayi iyaye da su ja wa ’ya’yansu kunne, da su guji wa amfani da abubuwan fashewa yayin bukukuwan domin duk wanda aka kama ya karya dokar zai fuskanci hukuncin hukuma.
Bola Longe, ya kara da cewa an ba ofisoshin rundunar a dukkanin yankunan jihar umarnin tabbatar da tsaro a lokutan bukukuwan.
Ya kara da bayar da lambobin tuntubar rundunar domin agajin gaggawa: 08112692680, 08108795930, 08037461715.