Bukayo Saka ya saka hannu kan yarjejeniyar mai tsawo da zai ci gaba da taka leda a Arsenal.
Dan wasan tawagar Ingila, ya ci kwallo 14 a Gunners a kakar nan, ya kuma bayar da 11 aka zura a raga.
- Dalilan da ke kai mata wajen bokaye
- DAGA LARABA: Yadda Rashin Sanin Kimar Waliyyai Ke Shafar Auratayya
Saka mai shekara 21 ya yi karawa 178 a kungiyar Emirates, ya kuma buga wa Arsenal dukkan wasannin Premier League a kaka biyu.
Tun farko kwantiragin Saka zai karkare a Arsenal a karshen kakar 2023-24, inda a yanzu ya tsawaita yarjejeniyar zuwa 2027.
Arsenal, wadda take ta biyu a teburin Firimiyar Ingila za ta karbi bakuncin Wolverhampton a wasan karshe a kakar bana.
Manchester City ce ta dauki kofin babbar gasar tamaula ta bana, bayan da Arsenal ta barar da damar lashe kofin kakar nan a karon farko tun bayan 2003/04.
Mikel Arteta ya ce zai yi kokari ya rike manyan ‘yan wasan Gunners, domin kalubalantar gasar zakarun Turai ta Champions League ta badi.