A makon jiya ne Mai martaba Sarkin Zamfarar Anka kuma Shugaban Majalisar Sarakuna ta Jihar Zamfara Alhaji Attahiru Muhammad Ahmad ya bukaci Gwamnatin Tarayya ta bai wa ’yan banga da sauran jami’an tsaron farin kaya bindigogi don yakar ’yan fashi da masu satar shanu a yankuna jihar.
Sarkin ya bayyana haka ne ranar Talata 4 ga Disamba 2018 lokacin kaddamar da rabon babura 850 ga sababbin ’yan kato-da- gora da aka horar ‘Cibilian Joint Task Force’ a jihar.
Alhaji Attahiru ya ce, ’yan fashi da makami da barayin shanu da masu garkuwa da mutane don neman kudin fansa suna yi wa jama’arsu kisan gilla. Jama’a da dama suna cikin matsala yayin da suke cikin mawuyacin hali a yanzu. Masu aikata irin wannan miyagun laifuffuka sun canja salon ayyukansu don haka ya zama wajibi hukumomi su ma su canja salon yakar wadannan miyagun laifuffuka.
Sarkin ya ce, “Noma da kiwon dabbobi da suka zama muhimman sana’o’in jama’ar jihar musamman makiyaya a yankunan karkara duk sun ajiye sana’o’insu saboda barayin da suka addabe su.
Ya shawarci iyalan wadanda aka yi garkuwa da su, su daina biyan kudin fansa, inda ya ce, duk wanda aka yi garkuwa da shi har ya mutu a hannun masu garkuwan ya yi shahada ne. Babban makamin da wadannan barayin ke amfani da shi, shi ne bindiga kirar AK47 yayin da su kuwa jama’ar da ake yi wa fashin ba su da komai sai dai sandar da suke kora dabbobinsu, don haka babu yadda za a iya hada bindiga da sanda.
Mai martaban ya ce, idan har gwamnati za ta amince da bukatarsu na samar musu da bindiga kirar AK47 tare da ba su lasisin mallakar makamai tabbas za su iya yin nasara a kan makiyansu.
Sarkin ya yaba da kokarin da gwamnatin jihar da hukumomin tsaro ke yi wajen horar da jami’an tsaron farin kaya na JTF tare da gargadin su da cewa, kada su dauki doka a hannunsu. Kwamishinan Kananan Hukumomi da Masarautu na Jihar Zamfara Bello Dankande Gamji, ya ce, doka ta tanadi wadanda ya kamata su mallaki bindigogi.
Sarkin Anka, ya bukaci gwamnati ta ba su izinin rike bindigogi don kare kansu daga barazanar barayin shanu da kuma dora wa Sarakuna nauyi sanadiyyar lamarin.
Kwamishinan ya yaba da hakurin wahalar da mutanen jihar ke sha da sauran masu rike da sarautu a kan wannan annoba ta fashi da makami da satar shanu da ke ci gaba da faruwa a yanzu shekara shida ke nan. Muna tunanin akwai hadari a bai wa wadansu mutanen jihar izinin rike bindigogi kamar yadda Sarkin ya bukata.
Amfani da makami ba kamar yadda aka tsara ba da wuce ka’ida wajen amfani da makamin tare da yawo da bindigogi suna cikin abubuwa uku da za su iya haifar da rashin bayar da lasisin bai wa kowa izinin rike bindiga. Wannan izinin za a iya bayar da shi ne a kasuwannin da suke sai da kananan makamai a kasar nan.
Misalin yaduwar bindigogi a kasar nan ba zai dakile rikicin da kasar ke fuskanta ba, har da na yankin Arewa maso Gabas da na yankin Neja Delta, ga rikicin manoma da makiyaya a Arewa ta Tsakiya, wanda ya haifar da annobar fashi da makami da yin garkuwa da jama’a don neman kudin fansa da kuma satar shanu musamman a yankuna Jihar Zamfara da wasu jihohin Arewa ta Yamma, duk wannan bai bai wa wadansu mahukunta damar rike makamai ba, don kare kansu.
Sakamakon yawaitar matsalar tsaro a Jihar Zamfara da wasu yankunan kasar nan akwai bukatar gwamnati ta inganta ayyukan ’yan sandan Najeriya. A makon jiya ne Rundunar ’Yan sanda ta rasa jami’anta 16 kuma ta ceto mutum 20 bayan wata arangama da suka yi da ’yan bindiga a Karamar Hukumar Birnin Magaji a Jihar Zamfara. Don magance artabu a tsakanin jami’an tsaro da masu laifi, hakan ya sa akwai bukatar a sanya dokar mallakar bindiga. A kasashen da suke da dokar rike bindiga wadanda suka mallake ta suna biyan kudi mai tsada saboda dokar.
A yayin da muke kara wa ’yan kasa kwarin gwiwar shiga harkar tsaro, muna kiran a hana barin makamai a hannunsu barkatai har da nufin rikewa don kare kansu. Wannan bukatar Sarkin za ta iya kawo wa shirin gwamnati cikas wajen ci gaban da take son samarwa. Kawai mafita ita ce a inganta ayyukan hukumomin tsaro da tabbatar da tsaron garuruwa da kauyuka da unguwanni daga annobar harin barayin shanu, wannan ba karamin abin takaici ba ne ga jama’ar Zamfara ba.