La’akari da irin barazanar da dagwalon masana’antun fata ke yi ga al’umma, Jami’ar Bayero ta Kano (BUK) ta kirkiri fasahar sarrafa shi zuwa takin zamani da kuma iskar gas.
Yunkurin dai a cewar jagoran shirin, kuma Daraktan Cibiyar Bincike da Kirkira ta Jami’ar, Farfesa Ibrahim Ahmad Rufa’i, wani hobbasa ne na tattaro masana, masana’antun fata, gwamnati da kuma jama’a don magance matsalar.
- A cikin ’yan Najeriya 10 mutum 9 ba sa iya cin lafiyayyen abinci
- Rashin tsaro: Mutanen Tsafe sun tare hanyar Gusau zuwa Funtua
Farfesa Ibrahim na jawabi ne yayin wani taron kara wa juna sani da jami’ar ta shirya da hadin gwiwar kamfanin fata na GB, Jami’ar Kimiyya da Fasaha ta Jihar Kano da ke Wudil da kuma kamfanin Royal Academy na kasar Birtaniya.
A cewarsa, “Fasahar da muka kirkiro za ta rika amfani da zafi ne wajen sarrafa dagwalon, har ya zama abin da muke bukata.
“Daga cikinsa, za mu sami iskar gas da kuma takin zamani. Ya zuwa lokacin da za mu kammala, muna fatan samar da sinadarin takin da ba shi da illa, wanda ko da mun yi amfani da shi a gonakinmu, ba zai lalata kasa ko amfanin da za mu noma ba.
“Mun jima muna tattauna matsaloli ba tare da kawo abin da ke haifar da su ko yadda za mu magance su ba.
“Amma ta hanyar tattaunawa irin wannan, za mu iya lalubo bakin zaren,” inji Farfesa Ibrahim.
A nasa bangaren, Shugaban Jami’ar ta Bayero, Farfesa Sagir Adamu Abbas, wanda Mataimakin Shugaban Jami’ar mai kula da bincike da ci gaba, Farfesa Abdullahi Sule Kano ya wakilta, ya ce yunkurin wani bangare ne na hobbasan da makarantar ke yi don magance matsalolin da suka addabi jama’a ta hanyar hada kai da sauran masu ruwa da tsaki.
Mahalarta taron dai sun fito ne daga makarantu da masana’antun fata da kuma gwamnati, a kokarin ganin an rage gurbata muhalli ta sanadiyyar dagwalon don bunkasa tattalin arzikin kasa.