✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Buhari zai yi saukin kayarwa a zaben 2019- Fayose

Gwamnan Jihar Ekiti, Ayodele Fayose ya ce maganar wai Buhari zai sake tsayawa takara rainin hankali ne ga ‘yan Najeriya, domin ya faza ta kowane…

Gwamnan Jihar Ekiti, Ayodele Fayose ya ce maganar wai Buhari zai sake tsayawa takara rainin hankali ne ga ‘yan Najeriya, domin ya faza ta kowane fannin mulki.

Gwamnan ya yi wannan bayanin ne jim kadan bayan Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya sanar da cewa zai sake tsayawa takara a zaben 2019.

“Idan har mutum ba zai iya gane ya kamata ya hakura ba, to ‘yan Najeriya za su fada masa ta hanyar kayar da shi a zaben 2019.

“Ba ma bukatar Buhari a matsayin shugaba. Ya tsufa kuma ya gaji. Ya kamata ya je ya huta. Sharinsa ya fi alherinsa yawa. Ya gaza a kowane fannin mulki, ta bangaren tattalin arziki ya gaza, ta fannin tsaro ma ya gaza domin kullum ana kashe mutane. ‘yan Najeriya sun gaji da shi, don haka maganar wai sake tsaywa takara rainin hankali ce kawai. Amma zai yi saukin kayarwa a zabe domin gwamnatinsa ta gaza.”