Shugaban Kasa Muhammadu Buhari zai halarci taron Kolin Shugabannin Kasashen Yankin Tekun Guinea da za a gudanar a Accra, babban birnin kasar Ghana.
Cikin wani sako da Fadar Gwamnatin Najeriya ta wallafa a shafinta na Twitter, ta ce Shugaba Buhari zai bar Najeriya ranar Talata 25 ga watan Afrilu domin halartar taron, wanda Shugaban Kasar Ghana Nana Akuffo-Ado zai jagoranta.
- Rikicin kabilanci ya ci mutum daya a Abuja
- Ana zanga-zangar adawa da gwamnatin Bashar al-Assad a Siriya
Ana sa ran Shugaba Buhari zai gabatar da jawabi a taron wanda zai tattauna dabarun karfafa zaman lafiya da tsaro da yaki da masu aikata miyagun laifuka a gabar tekun yankunan kasashen.
Yayin halartar taron, shugaban zai samu rakiyar Ministan Harkokin Wajen harkokin Kasashen Wajen, Geoffrey Onyeama, da Mai Bai wa Shugaban Kasa Shawara kan Harkokin Tsaro, Babagana Monguno mai ritaya.
Sauran wadanda za su rufa wa Buhari baya sun hada da Daraktan Hukumar Tattara Bayanan Sirri (NIA), Ambasada Ahmed Rufai Abubakar, da sauran jami’an gwamnati.