✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Buhari zai tafi Ghana ranar Lahadi

Buhari zai halarci wani taron gaggawa da kungiyar ECOWAS ta kira.

A gobe Lahadi ake sa ran Shugaba Muhammadu Buhari zai bar Abuja zuwa Accra, babban birnin Kasar Ghana domin halartar wani taron gaggawa da kungiyar ECOWAS ta kira kan rikicin siyasar da ya dabaibaye kasar Mali.

Sanarwar hakan na kunshe cikin wani sako da Fadar Gwamnatin Najeriya ta wallafa a shafinta na Twitter da yammacin ranar Asabar.

“A yayin da al’amura suke ci gaba da gudana, Shugaba Buhari yana Allah wadai da juyin mulkin da sojoji suka yi ranar 24 ga watan Mayu a Mali.
“Kazalika, shugaban ya yi tir da kama Shugaban kasar da Firaiministansa da sojoji suka yi.

“Yana kuma kira da a gaggauta sakin dukkanin jami’an gwamnatin na farar hula da ke tsare,” a cewar sanarwar.

Shugaban kungiyar ci gaban tattalin arzikin kasashen Yammacin Afirka kuma Shugaban Ghana, Nana Akufo-Addo ne zai jagoranci taron kamar yadda sanarwar ta bayyana.

Tawagar Shugaba Buhari za ta kunshi Ministan Harkokin Wajen Najeriya; Geoffery Onyeama, Ministan Tsaro; Manjo-Janar Bashir Salihi Magashi (mai ritaya); Ministan Masana’antu, Kasuwanci da Zuba Jari; Otunba Richard Adebayo da kuma Daraktan Hukumar Leken Asiri (NIA); Ahmed Rufai Abubakar.

Aminiya ta ruwaito cewa, a Juma’ar da ta gabata ce Shugaba Buhari ya karbi bakuncin tsohon Shugaban Kasa Goodluck Jonathan inda suka tattauna kan rikicin siyasar kasar Mali kasancewarsa jakada na musamman na Najeriya kuma mai shiga tsakanin rikicin.