Jam’iyyar APC ta yi kira ga Gwamnatin Tarayya da ta gaggauta sanya dokar ta-ɓaci a Jihar Ribas sanadiyyar rikicin siyasar da ya ƙi ci ya ƙi cinyewa.
Jam’iyar ta kuma buƙaci da a tura sojoji da makamai a girke su a wurare na musamman a jihar domin kare abin da ta kira ɓarkewar rikici.
- Yadda ’yan wasan Super Eagles suka kunyata ’yan Nijeriya
- Sabon taken Najeriya zai magance matsalar ta’addanci —Akpabio
Shugaban kwamitin riƙo na jam’iyyar APC a Ribas, Cif Tony Okocha ne ya yi wannan kiran yayin ganawa da manema labarai a Fatakwal a ranar Laraba.
Ya ce, “Jihar Ribas na fama da yaƙi, kuma wannan rikicin siyasa ne ke da alhakin tashe-tashen hankulan da suka yi sanadin salwantar rayuka da ba a san adadi ba.
“Gwamnan ya ƙi ɗaukar mataki, ‘yan sanda ba su ba da wani taimako. Don haka ya kamata a sanya dokar ta-baci a Jihar Ribas a matsayin hanyar da za ta magance tarzoma da tada zaune tsaye a jihar.
“Ina kira ga gwamnatin tarayya da ta gaggauta ɗaukar mataki kan wannan lamarin.”
Muna Allah wadai da abin da ke faruwa a Ribas — ’Yan sanda
Sufeto janar na ’yan sandan Nijeriya ya yi tir da kisan jami’an rundunar da aka yi a Jihar Ribas sakamakon rikicin siyasar da ke cigaba da ruruwa tsakanin Gwamna Siminalayi Fubara da tsohon Gwamna Nyesom Wike.
Wata sanarwa da kakakin rundunar, Olumuyiwa Adejobi, ya fitar ta ce IGP Kayode Egbetokun ya bai wa kwamashinan ’yan sandan jihar umarnin tsaurara tsaro don gano waɗanda suka aikata kisan.
Sanarwar ta ce an kashe Sufeto David Mgbada da kuma wani ɗan sa-kai Samuel Nwigwe a rikicin da ya auku tsakanin magoya ɓangarorin biyu bayan Gwamna Fubara ya rushe shugabannin ƙananan hukumomi tare da maye gurbinsu da na riƙo.
“Sakamakon haka, IGP ya aika da dakarun rundunar na Intelligence Response Team (IRT) domin su taimaka wa ’yan sandan Ribas wajen kama makasan,” in ji sanarwar.
Aminiya ta ruwaito cewa a yau Laraba ne gwamnan ya rantsar da shugabannin bayan tun da farko majalisar dokokin jihar, ɓangaren da ke biyayya ga gwamnan, ya tantance mutanen.