✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Buhari zai tafi Amurka ranar Lahadi

Buhari zai gabatar da jawabi a taron da shugabannin kasashen duniya za su halarta.

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari zai yi balaguro zuwa kasar Amurka a ranar Lahadi.

Hakan na kunshe ne cikin sanarwar da Babban Hadimin Shugaban Kasar kan Kafofin Sadarwar Zamani, Bashir Ahmad ya wallafa a shafinsa na Twitter a wannan Asabar din.

Bashir Ahmad ya ce Buhari zai ziyarci Amurka ce domin halartar Babban Taron Majalisar Dinkin Duniya na shekara-shekara karo na 77 da za a gudanar a birnin New York.

Sanarwar ta ce shugaban zai gabatar da jawabi a ranar Laraba a taron da shugabannin kasashen duniya za su halarta.

Wannan na zuwa ne yayin da Mataimakin Shugaban Kasa, Farfesa Yemi Osinbajo ya tafi wakiltar Najeriya a jana’izar Sarauniya Elizabeth II da za a gudanar ranar Litinin a Birtaniya.