✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Buhari zai sa hannu kan kasafin kudi ranar Talata

Hadimin Shugaban Kasa Kan Kafofin Yada Labarai na Zamani, Bashir Ahmad, ya ce, Buhari zai sanya hannu kan kasafin ne a Fadar Shugaban Kasa.

Fadar Shugaban Kasa ta ce a ranar Talata Shugaba Muhammadu Buhari zai sanya hannu a kan kasafin kudin shekarar 2023 da muke ciki.

Hadimin Shugaban Kasa Kan Kafofin Yada Labarai na Zamani, Bashir Ahmad, ya ce, Buhari zai sanya hannu kan kasafin ne a Fadar Shugaban Kasa.

Shugaban Kasa zai rattaba hannu kan kasafin ne bayan amincewar Majalisar Dokoki ta Kasa, wadda ta kara Naira tiriliyan 1.3 a kan abin da shugaban kasar ya gabatar mata na tiriliyan N20.5.

Sanya hannu kan kasafin na zuwa ne a ranar da aka dawo daga hutun bikin shiga Sabuwar Shekara.

Bayan hawan Buhari mulki ne dai Najeriya ta koma aiwatar da kasafin kudinta na shekara daga watan Janairu zuwa Disamba, wanda kafin shi hakan na gagara.

A makon jiya Aminiya ta kawo rahoton Amincewar Majalisar Wakilai da kasafin bayan kara yawansa zuwa Naira tiriliyan 21.8 daga tiriliyan N20.5 da shugaban kasa ya gabatar mata a watan Oktoba.

Jimillar kasafin ya nuna an ware tiriliyan N6.55 domin biyan basuka, tiriliyan N8.3 domin ayyukan yau da kullum.

An ware biliyan N967.48 domin hukumomi da ma’aikatun gwamnati sai kuma tiriliyan N5.97 domin manyan ayyuka, daga ranar 1 ga watan Janairu zuwa 31 ga watan Disamba 2023.

Waiwaye

Da yake bayani kan Kasafin Kudin na 2023 a watan Oktoban 2022, Shugaba Buhari ya ce daga cikin Naira tiriliyan 20.51 da za a kashe, za a yi amfani da Naira triliyan 6.557 wajen biyan basuka.

Yadda za a kashe kudin a dunkule:

 • Ayyukan Yau da Kullum:  Naira tiriliyan 8.271.
 • Biyan Basuka: Naira tiriliyan 6.557.
 • Manyan Ayyuka: Naira tiriliyan 4.934.
 • Hukumomin Gwamnati: Niliyan N722.109.

Ma’aikatu masu kaso mai tsoka

Daftarin kasafin ya kuma nuna bangaren tsaro ne ya fi samu kaso mai tsoka, inda aka ware masa Naira tiriliyan 1.091, sai Ilimi a matsayi na hudu da Naira biliyan 663.971, sai lafiya mai Naira biliyan 508.8; a yayin da Ma’akatar Noma ta zo a matsayi na 10 da Naira biliyan 85.4.

Jerin ma’aikatu da hukumomi 10 masu kaso mafi tsoka:

 1. Tsaro – Tririliyan N1.1.
 2. Albashi – Biliyan N921.1.
 3. Harkokin ’Yan Sanda – Biliyan N777.4.
 4. Ilimi – Biliyan N663.971.
 5. Lafiya – Biliyan N580.8.
 6. Harkokin Cikin Gida – Biliyan N277.7.
 7. Wasanni da Matasa – Biliyan N187.1.
 8. Mashawarci kan Tsaro – Biliyan N166.
 9. Harkokin Waje – Biliyan N93.4.
 10. Noma da Raya karkara – Biliyan N85.4.

Buhari ya ware N470b domin inganta jami’o’i

Haka kuma shugaban ya ware Naira biliyan 470 domin samar da kayan aiki da inganta karatu a jami’o’i a kasafin na 2023.

Idan ba a manta ba, a kwanakin baya Kungiyar ASUU din da ke bukatar Naira triliyan 1.2, ta yi watsi da tayin ware wa jami’o’in Naira biliyan 150 da gwamnatin ta ce za ta ware mata a rubu’i na farko a kasafin na badi.

Ya ce gwamnatinsa ba ta sanya hannu a yarjejeniyar da yake da yakinin cewa ba za su iya cikawa ba.

Ya kara da cewa gwamnati kadai ba za ta iya magance matsalolin bangaren ilimi ba, inda ya ce: “A kasashe da dama, harkar ilimi na rataya ne a hadakar tsakanin gwamnati da mutane, musamman ma karatun manyan makarantu.”

Kasafin shekara 7 da suka gabata a sikeli

Masana tattalin arziki sun bayyana cewa a kasafin kudi bakwai da Shugaba Buhari ya gabatar a baya masu gibi ne, ta yadda abin da ake shirin kashewa ya zarce kudaden shiga da gwamnati ke hasashen samu a shekara.

Abubakar Aliyu, masanin tattalin arziki kuma jami’in huldar hada-hadar hannun jari ya ce, idan aka yi kasafi mai gibi, to sai an nemo ko an ciyo bashi domin kudaden da za a cike gibin da aka samu.

Dalilin da Buhari ke yin kasafi mai gibi

Farfesa Garba Ibrahim Sheka na Jami’ar Bayero ta Kano ya ce, “Tun da Buhari ya zo, kudin da ake samu [a gwamnati] bai kai wanda ake kashewa ba saboda haka duk shekara sai ka ji za a karbo bashi saboda za a cike gibin kasafin kudi.”

Ya ce Buhari yana irin wannan kasafi ne bisa fahimtar mazhabar tattalin arziki da ke ganin ita ce hanyar bunkasa tattalin arziki.

“Idan Allah Ya sa an dora kasafin a kan bangarorin tattalin arziki da za su kawo cigaba da bunkasa masana’antu da harkar noma da sauransu, wadanda su ne idan an bunkasa su arziki zai rika zagayawa [tsakanin jama’a].

“Idan ka tabbatar za ka samu Naira 100 sai ka yi lissafin Naira 150, to idan ka samu Naira 120, to ka ga Naira 20 da ta shigo ba ta cikin lissafinka, jajircewarka da takura wa kanka ne ya sa ka samu.”

Amma ya ce, irin wannan kasafi da bashi ake cike shi, domin daga karshe kasafin da aka yi doka yake zama, don haka sai an aiwatar da shi.

“Hakan ne ya kai kasar ga halin irin bashin da ke kanta yanzu.”

‘Bashi ya durkusar da Najeriya’

Abubakar Aliyu ya ce, shi ya sa “Tun da farko mun yi mamakin ganin ana kasafi na tiriliyoyin Naira, alhali kasar ba ta iya samun wadannan kudade.

“To a hankali ana cike gibin nan da basussuka, har yanzu aka kai ga a shekara bakwan nan, basussukan da aka rika karba ana cikin gibin sun zo sun durkusar da kasar.

“Hakan ya sa a rubu’in farko na wannan shekara, an biya bashi da kudaden da muke samu a cikin gida, har ma sai da aka kara da ciyo bashi na kashi 120 cikin 100,” inji masanin tattalin arzikin.

Ya bayyana cewa a tsawon shekara bakwai da suke gabata, “abin tsoro shi ne kudaden da aka ciyo bashi domin manyan ayyyuka, zan iya cewa ba a yi ayyukan ba kuma kudaden babu su.

“Na san bashin da aka karba na Dala biliyan 5.5 a hanyar sayar da hannun jarin Euro Bond, domin gyara tashar wutar lantarki ta Mambilla da gyaran filayen jiragen sama da biyan ’yan kwangila.

“Amma daga baya Ministan Lantarki ya fito yana cewa ko share filin ba a yi ba.”

Bangaren da ya fi samun kaso

Masanan sun bayyyana cewa, bangarorin tsaro da manyan ayyyuka da abubuwan more rayuwa da noma da masana’antu su ne suka fi samun kaso mai tsoka a kasafin shekara bakwai da suka gabata.

Farfesa Sheka ya ce, Buhari ya ba da fifiko a kan bangaren noma ne saboda “ana so a ciyar da kai.

“An rufe boda saboda a irin karfin da za a iya noma shinkafa da sauran abubuwa.

“An fito da abubuwa da dama, kamar ba wa manoma wani bashi kyauta-kyauta, wanda bankin CBN ya jagoranta,” a cewar Farfesa Sheka.

A cewar Abubakar, wani bangaren da ya samu kaso mai tsoka, shi ne bangaren gudanar da gwamnati, wanda a cewarsa bai kamata ba.

“Yaya za a yi ka karbi basuka ka yi wananna abubuwan da su?”

Bangaren tsaro ya samu kaso mai tsoka ne saboda matsalolin da kasa ke fuskanta ta wannan bangare, kama daga ta’addancin Boko Haram zuwa ’yan bindiga da ’yan aware da sauransu.

Batun manyan ayyuka kamar yadda suka bayyana, ya samu kaso mai yawa ne saboda ayyukan gina titunan jirgin kasa da hanyoyi mota, “wadanda ga su nan ana ta yi.”

Shin ko kwalliya ta biya kudin sabulu?

Abubakar Aliyu ya ce kwalliya ba ta biya kudin sabulu ba a kasafin shekara bakwai da suka gabata.

Yaki da talauci

Game da tsarin bayar da rance ko tallafi, ya ce: “Abin mamaki shi ne, babu wani tsari na cewa za a yi yaki da talauci.

“Yaki da talauci ba wannan hanya za a bi ba. Yaya za ku bai wa mutane kudi, ba ku tura su wurin sana’a ba? Wannan, idan ma kudaden na isa hannunsu ke nan,” inji shi.

Bangaren Noma

Farfesa Sheka ya ce akwai sauran rina a kaba a bangaren noma, domin duk da tallafi da rance da sauran matakan da gwamnati ta dauka kan ganin an ciyar da kai.

“Sai ya zama wadda ake nomawa a gidan na ta neman ko ma ta fi ta wajen tsada, ko kuma suna kan-kan-kan.

“Ka ga a iya cewa ba a ci nasara ba, domin ana noma ta a gida amma farashi bai sauka ba, sai dada hauhauwa ma yake, har ana maganar da za a bude boda a shigo da ta wajen, talakawa su samu sauki, da ya fi.”

Manyan ayyuka

Game da abubuwan more rayuwa, malamin jami’ar ya bayyana cewa hakika ana yi.

“Amma more rayuwar ba ta zo ba saboda amfanin mutun ya gina abu shi ne ya yi amfani da shi.”

Amma a cewarsa, duk da cewa Buhari ya dora a kan gina titin jirgin da Gwamnatin Jonathan ta fara kuma yana gina tituna, rashin tsaro a kan hanyoyin sufurin tamkar an yi baya babu zani ne.

Kasafin 2023

Da yake hasashen abin da kasafin 2023 zai kunsa, Abdullahi Aliyu ya ce, yana ganin ba za ta sauya zane ba, lura da abin da aka saba gani a kasafin shekara bakwai da suka gabata.

Sai dai ya ce babu mamaki, “A kara wa bangaren zartarwa kaso saboda bukatun gudanar da gwamnati da na siyasa, kamar yin zabe da sauransu.”

%d bloggers like this: