Shugaba Buhari zai rattaba hannu a kan sabon kasafin kudin 2020 da Majalisar Tarayya ta amince da shi a watan Yuni.
Fadar Shugaban Kasa ta shafinta na Twitter ta ce Shugaba Buhari zai rattaba hannun ne a ranar Juma’a 10 ga watan Yuli, 2020.
A rana 13 ga watan Maris ne Gwamantin Tarayya ta amince da sabon kasafin da aka rage zuwa Naira tiriliyan 10.523 da Ma’aikatar Kudi da tsare-tsaren Kasa ta gabatar wa Majalisar Zartaswarsa ta Kasa.
Sabon kasafin na kuma dauke da sauye-sauyen da aka yi wa kasafin kasa na matsakaicin zango daga 2029.
Da farko Shugaba Buhari a watan Disamban 2019 ya fara amincewa da kasafin 2020 na Naira tiriliyan 10.59 wanda ya sami amincewar Majalisar.
Da farko Majalisar ta amince da kasafin ne da aka yi a kan hasashen farashin gangar danyen mai $57.
Daga baya Gwamantin Tarayya ta rage kasafin saboda faduwar farashin mai sakamakon annobar coronavirus.