Ministan watsa labarai, Alhaji Lai Mohammed ya tabbatar da cewar za a gudanar da taron majalisar ministocin na karshe ne a ranar 22 ga watan Mayu 2019. Wanda hakan ke nufin shugaba Buhari zai yi bankwana da ministocin na sa a wannan rana.
Taron zai gudana ne mako guda kacal, gabanin a sake rantsar da shugaba Buhari a wa’adi mulki na biyu.
Wakilinmu ya fahimci cewa, tun bayan da shugaba Buhari ya bukaci ministocin na sa da su gabatar da cikakken bayanin yadda suka gudanar da ayyukan ma’aikatunsu daban-daban, tun lokacin ne aka fara rade-radin mai yiwu ne shugaban ya rushe majalisar ministocin na sa.