✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Buhari zai karbo bashin Dala miliyan 800 daga Bankin Duniya

Buhari na fatan ganin an rage radadin da za a fuskanta saboda cire tallafin man fetur.

Shugaba Muhammadu Buhari na neman amincewar Majalisar Dattawa domin karbo bashin Dala miliyan 800 daga Bankin Duniya.

Hakan na kunshe ne cikin wata wasika da Shugaban Majalisar Dattawan ya karanta yayin zaman majalisar a ranar Talata.

Wasikar Shugaban Kasar ta yi bayanin cewa za a ciyo bashin ne domin rage radadin da za a fuskanta bayan sanadiyar tallafin man fetur da za a cire.

Ana iya tuna cewa, wata sanarwa da Gwamnatin Tarayya ta fitar a watan Afrilu ta bayyana cewa, tallafin dala miliyan 800 na Bankin Duniya za a yi amfani da shi ga ’yan Najeriya masu rauni su miliyan 50 ko gidaje miliyan 10.

A cewar Ministar Kudi da Kasafi da Tsare-Tsare, Zainab Ahmad, za a rarraba tallafin ne bisa shirin da aka yi na cire tallafin mai a watan Yunin bana.

Ministar ta ce ana ci gaba da aiki tare da sabon kwamitin mika mulki na Shugaban Kasa da gwamnati mai jiran gado domin tafiyar da shirin da ya hada da bukatar samar da bas-bas da wasu bukatu da dama.

Wannan yunkuri na karbo bashin na zuwa ne a daidai lokacin da Buhari ke shirin mika mulki a ranar 29 ga wannan wata na Mayu ga magajinsa, Bola Ahmed Tinubu da ya lashe Zaben Shugaban Kasa a cikin watan Fabrairun da ya gabata.