✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kotu ta samu Donald Trump da laifin cin zarafin mace

Trump dai ya ce shari’ar bita da kullin siyasa ce, yana mai cewa sam bai san matar ba.

Kotu ta umurci tsohon Shugaban Amurka,  Donald Trump ya biya matar da aka tabbatar ya ci zarafinta ta hanyar neman yin lalata da ita shekaru da dama da suka wuce, lamarin da Trump ya sha musantawa a baya.

Wata babbar kotu da ke zama a birnin New York a ranar Talata, ta umurci Trump ya biya matar mai ba da shawarwari a wata mujalla dalar Amurka miliyan biyar ($5,000,000).

Lamarin na zuwa ne bayan kammala sauraron bahasi da suka tabbatar da Trump ya aikata laifin cin zarafin matar ta hanyar yin lalata da ita shekaru 20 kafin ya zama shugaban kasa.

Masu shari’a su tara da suka hada da maza 6 mata 3, sun yanke wannan hukuncin ne bayan shafe sa’a uku suna shawara.

Wannan shi ne karo na farko da Trump zai fuskanci tuhumar da aka same shi da laifi bayan kwashe shekaru yana fuskantar tuhume-tuhume daga matan da suke zargin shi da yin lalata da su.

Masu shari’ar sun yi watsi da zargin da E. Jean Carroll wacce yanzu take da shekaru 79, kan cewa Trump ya yi lalata da ita a dakin canza kaya na wani katafaren shagon sayar da tufafi a New York a shekarar 1996.

Amma kuma, sun yanke cewa ya ci zarafinta kana suka umurce shi da biyanta dalar Amurka miliyan 2 akan wannan zargin.

Sun kuma umurce shi da biyan Carroll dalar Amurka miliyan biyar a dalilin Trump ya yi ta musa tuhumar da ta yi mishi ta kafar sada zumunta.

Daga bisani, Caroll ta fitar da wata sanarwa inda ta ce, “na shigar da karar Trump ne domin na wanke kaina kuma na ceto mutunci na.

“Yau dai gaskiya ta yi halinta kuma duniya ta san gaskiyar lamarin.

“Wannan ba nasara ta ba ce ni kadai amma nasarar kowace macen da ta fuskanci wani cin zarafi a hannun Trump ne kana a ka ki yarda da ita.”

Trump dai ya ce shari’ar bita da kullin siyasa ce, yana mai cewa sam bai san matar ba.