Ministan Ayyuka da Gidaje, Babatunde Fashola, ya ba da tabbacin cewa Shugaban Kasa Muhammadu Buhari zai kammala tare da kaddamar da titin Kano zuwa Kaduna kafin ranar 29 ga watan Mayu, 2023.
Sai dai ya ce za a ci gaba da aiki a bangaren Kaduna zuwa Abuja na hanyar ko da bayan karewar wa’adin Shugaban, saboda ba za a sami tangarda wajen biyan kudin aikin ba.
- Fada ya barke tsakanin ’yan banga da sojoji a Ribas
- Babu lallai a ga jinjirin watan Shawwal a ranar Alhamis —Masana
Ya bayyana hakan ne a Zariya, ranar Litinin, lokacin da ya jagoranci tawagar Gwamnatin Tarayya domin ziyarar gani da ido a titin, a shirye-shirye kaddamar da shi a watan na gobe.
A cewarsa, “Mun yi alkawarin kammala wannan aikin kafin karewar wa’adin gwamnati, kuka cikin ikon Allah za mu cika shi.
“Bangaren Kaduna zuwa Zariya, wanda ke da nisan kilomita 73, ’yan kwangila sun ba mu tabbacin za a kammala shi kafin karshen makon nan, yayin da Zariya zuwa Kano kuma a wata mai zuwa,” in ji Fashola.
Da aka tambaye shi makomar aikin Abuja zuwa Kaduna bayan wa’adin Buhari, Ministan ya ce aikin zai ci gaba saboda Asusun Hukumar Zuba Jari ta Najeriya ne ke kula da samar masa da kudade, kuma zai ci gaba ko da wane ne yake Shugaban Kasa.
Ya ce daga cikin kalubalen da ya jawo wa aikin na Abuja zuwa Kaduna tsaiko akwai matsalar tsaro da ta biyan diyya da kuma matsar da turakun lantarki.
Tun da farko da yake nasa jawabin, Shugaban Ma’aikatan Fadar Shugaban Kasa, wanda shi ma yake cikin tawagar, Farfesa Ibrahim Gambari, ya ce aikin hanyar yana daya daga cikin manyan ayyukan da gwamnatin Buhari ke tunkaho da su.
Ya ce an saka ayyukan ne a Asusun Shugaban Kasa na Ayyukan Raya Kasa kuma dukkansu za a kammala su kafin ya sauka daga mulki.
Yayin ziyarar, Ministan ya sami rakiyar Hadimin Shugaban Kasa kan Harkokin Majalisar Tarayyar, Nasiru Baballe Ila.