✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Buhari zai je London bikin nadin Sarkin Ingila

A yau Shugaba Muhammadu Buhari zai yi bulaguro domin halartar bikin nadin Sarki Charles III da matarsa Camilla.

A yau Shugaba Muhammadu Buhari zai yi bulaguro zuwa kasar Birtaniya domin halartar bikin nadin Sarki Charles III da matarsa Camilla.

Buhari wanda zai samu rakiyar manyan jami’an gwamnatinsa, yana daga ciki shugabannin duniya da Fadar Burkingham ta Birtaniya gayyata domin halartar bikin da zai gudana ranar Asabar, 6 ga watan Mayu.

Kakakin shugaban kasa, Femi Adesina ya ce gabanin bikin nadin Sarki Charle III, Kungiyar Kasshe Rainon Ingila za ta gudanar da babban taronta a ranar Juma’a 5 ga wata.

Taron, wanda Buhari zai halarta zai tattauna da kan makomar kasashen da muka rawar da matasa za su taka.