Shugaba Muhammadu Buhari zai jagoranci wani taron gaggawa na Majalisar Magabata a ranar Juma’a mai zuwa 10 ga watan nan na Fabrairu.
Taron zai tattauna ne a kan matsalolin da kasar ke fama da su a yanzu da suka hada da karancin man fetur da na takardun Naira da matsalar tsaro yayin da kasar ke fuskantar babban zabenta da za a fara ranar 25 ga watan nan nan Fabrairu.
- NHRC za ta binciki ayyukan sojoji a Arewa maso Gabas
- Kotun Koli ta dakatar da aiwatar da wa’adin tsohuwar Naira
Halin da kasar ke ciki na wadannan matsaloli musamman karancin Naira da kuma matsalar mai sun sa an fara zanga-zanga a wasu sassan kasar da dama.
Aminiya ta ruwaito cewa, ana sa ran gwamnan Babban Bankin Najeriyar, Godwin Emefie zai yi wa majalisar bayani a yayin taron da zai gudana a Fadar Gwamnatin Najeriya da ke Abuja, game da batun canjin kudin kasar, lamarin da ya jefa al’umma da dama cikin halin kaka-ni-kayi.
Haka kuma wasu majiyoyo a fadar shugaban na cewa shugaban Hukumar Zabe ta Kasa INEC, Farfesa Mahmood Yakubu, da Babban Sufeton ’Yan sanda Usman Alkali Baba za su yi wa majalisar bayani kan shirye-shiryen zaben Shugaban Kasa da na ’yan Majalisar Tarayya da za a yi ranar 25 ga watan na Fabrairu da kuma na gwamnoni da ’yan majalisar jiha da za a yi ranar 11 ga watan Maris.
Majalisar Magabatan ta kunshi shugaban kasar da mataimakinsa da Sakataren Gwamnatin Tarayya da tsofaffin shugabannin kasa da tsofaffin manyan alkalan kasa da shugaban Majalisar Dattawa da shugaban Majalisar Wakilai da gwamnonin jihohi 36 da kuma babban lauyan gwamnati kuma Ministan Shari’a.