✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Buhari zai halarci daurin auren dansa ranar Juma’a

Za a fara gudanar da shagulgulan bikin a ranar Alhamis.

Masarautar Bichi ta sanar da cewar Shugaban Kasa Muhammadu Buhari na daga cikin manyan bakin da ake sa ran za su yi wa garin Bichi tsinke, don halartar daurin auren dansa, Yusuf da Zahra, ‘ya ga Sarkin Bichi.

Madakin Bichi, Alhaji Nura Shehu Ahmad wanda shi ne shugaban kwamitin gudanar da shirye-shiryen bikin, ya ce za fara gudanar da shagulgulan bikin daga ranar Alhamis.

Ya ce bikin zai fara da addu’a ta musamman a babban masallacin garin Bichi da misalin karfe 3:30 na yammacin ranar Alhamis.

Daga nan kuma sai a dunguma zuwa babban dakin taro na Kwalejin Ilimi ta Tarayya da ke Bichi, inda za a gudanar da lakca da misalin karfe 4 na yamma.

Za a daura auren da misalin karfe 1:30 na yammacin ranar Juma’a, yayin da za a yi shagalin bikin nadi a ranar Asabar da misalin karfe 9:30 na safe a filin wasa na garin Bichi.

Ya ce kwamitin tsaro ya shirya tsaf don tabbatr da ingantaccen tsaro a yayin bikin, inda za a girke jami’an tsaro da suka hada da ma’aikatan hukumar tsaro ta farin kaya (DSS), hukumar tsaro ta farin kaya da farar hula (NSCDC), Hisbah, da kuma ‘yan banga karkashin jagorancin tsohon kwamishinan ‘yan sanda Shehu Kabiru Bayero.

Kazalika, ya ce an ware wani karamin kwamiti da zai ke lura da bin matakan kariya daga cutar COVID-19.

Idan za a iya tunawa akalla gwamnoni bakwai ne suka ziyarci fadar Sarkin Kano, Alhaji Aminu Ado Bayero, don yin baikon auren dan shugaban kasa da gimbiyar masarautar Bichi.