✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Buhari zai gana da duk Sanatoci 109 a daren Talata

Buhari zai gana da Sanatocin da misalin karfe 8:00 na dare.

Shugaba Muhammadu Buhari a daren yau na Talata zai gana da duk Sanatoci 109 a Fadar Gwamnatin Najeriya da ke Abuja, babban birnin kasar.

Ganawar da Buhari zai yi tare da Sanatocin da misalin karfe 8 na dare na kunshe cikin wata sanarwa da hadimin Shugaban Majalisar Dattawa, Ezrel Tabiowo ya fitar.

Sanarwar ta ce hakan na kunshe ne cikin wata wasikar gayyata da Shugaban Kasar ya aike wa Majalisar Dattawa, kuma aka karanta wa mambobinta yayin zaman majalisar na ranar Talata.

A cewar wasikar da Shugaban Majalisar, Sanata Ahmad Lawan ya karanta, “Shugaban Kasar yana gayyatar dukkan Sanatoci zuwa wata liyafar dare da aka shirya da misalin karfe 8:00 na daren Talata, 13 ga watan Yuli.

“Wurin da za a gudanar da wannan liyafa shi ne dakin taro na Banquet Hall da ke Fadar Gwamnatin Najeriya a Abuja,” a cewar wasikar.

Tun a ranar 27 ga watan Afrilun da ya gabata ne Majalisar ta cimma matsayar neman ganawa da Shugaban Kasar, domin bai wa Sanatocin damar tattaunawa a kan kalubalen da suka addabi kasar musamman matsalar tsaro.