Wasu daga cikin Sanatocin Najeriya, sun bayar da gudunmawar Naira miliyan 74 don tallafa wa mutanen da ambaliyar ruwa ta shafa a Maiduguri, Babban Birnin Jihar Borno.
Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Barau I. Jibrin ne, ya bayyana hakan a madadin Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Godswill Akpabio, lokacin da ya jagoranci wasu ’yan majalisar zuwa Maiduguri a ranar Talata.
- Ambaliya: Fursunoni 281sun tsere a Maiduguri — NCS
- Duk da tsadar rayuwa an sami ƙaruwar masu Zagayen Maulidi a Gombe
Sanata Barau, ya ce kowane daga cikin Sanaroci 108 zai bayar da Naira 500,000, wanda zai kama Naira miliyan 54.
Haka kuma ya bayar da tallafin Naira miliyan 10 ta shi ta kansa.
Ƙungiyar Sanatocin Arewacin Najeriya ma, ta bayar da tallafin Naira miliyan 10, wanda ya haɗa jimillar tallafin zuwa Naira miliyan 74.
Sanatocin da suka ziyarci Maiduguri, sun haɗar da Shugaban Ƙungiyar Sanatocin Arewacin Najeriya, Sanata Abdulaziz Musa Yar’Adua, Shugaban Ƙungiyar Sanatocin Kudancin Najeriya, Sanata Mukhail Adetokunbo Abiru, Sanata Ikra Aliyu Bilbis, Sanata Onawo Mohammed Ogoshi, Sanata Sadiq Suleiman Umar da sauransu.
Sanata Barau, ya miƙa ta’aziyyarsa a madadin Majalisar Dattawa ga waɗanda ambaliyar ruwa ta shafa, tare da yi musu addu’a.
Ya ce, “Mun zo nan domin miƙa ta’aziyyarmu ga gwamnatin Jihar Borno da kuma ɗaukacin al’ummar jihar. Abin da ya shafi Borno ya shafi ƙasa baki ɗaya.”
Kazalika, Sanatocin sun kai ziyarar ta’aziyya ga tsohon Sanata Baba Kaka Garbai, wanda ya wakilci Borno ta Tsakiya a Majalisar Dattawa ta Takwas, sakamakon rasuwar mahaifiyarsa a makon da ya gabata.