A mako mai zuwa ake sa ran Shugaba Muhammadu Buhari zai gabatar da daftarin kasafin kudin shekara mai zuwa a gaban zaman tare na Majalisun Tarayyar kasar biyu.
Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Ahmad Lawan ne ya bayyana hakan a ranar Talata yayin da gabatar da sakonsa na barka da dawo wa daga hutun shekara ga ‘yan majalisar.
- Gwamnatin Najeriya ta ba da hutun aiki ranar Alhamis
- Dalilin da ya sa ba za a janye wa Mali takunkumi ba – Buhari
Kamar dai yadda kasance a bara, Gwamnatin Tarayya na hanzarin shigar da kasafin kudin kasar cikin doka domi tabbatar da tsarin kasafin daga Janairu zuwa Dasumba.
Da wannan ne Shugaban Majalisar Dattawan ya ke cewa za a bai wa Ma’aikatu, Cibiyoyi da Hukumomin Gwamnati wa’adin wata guda domin su gabatar da dalilai da hujjojin kudin da za su kashe a badi kamar yadda ya ke rubuce a kasafin da Shugaban Kasar zai gabatar.