Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya mika sunayen mutum bakwai domin nada su ministoci a gwamnatinsa.
Hakan na kunshe ne a cikin wata wasikar Shugaban Kasar da aka ka karanta a zauren Majalisar Dattawa a ranar Talata.
- Masu garkuwa da mutane 13 sun shiga hannu a Adamawa
- Adamu ya yi watsi da zargin sayen kuri’a a Zaben Ekiti
A wasikar da Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Ahmad Lawan, ya karanta, Buhari ya bukaci Majalisar ta gaggauta nazari da kuma amincewa da mutanen da ya mika sunayensu.
Buhari ya gabatar da sunayen ne bayan gibin da aka samu a gwamnatinsa, tun bayan da ya sallami wasu daga cikin ministocinsa a watannin baya.
Bayan nan kuma wasu karin ministocinsa sun yi murabus daga mukamansu domin tsayawa takara a zaben 2023 da ke kara matsowa.
Daga cikin ministocin da suka sauka daga mukamansu domin neman takarar shugaban kasa a jam’iyyar APC mai mulki har hada da Chubuike Rotimi Amaechi, Ministan Sufuri da takwaransa na Ma’aikatar Ilimi, Chukwuemeka Nwajiuba da kuma Ministan Kimiyya da Fasaha, Ogbonnaya Onu da kuma Ministan Neja Delta, Godswill Akpabio.
Daga cikin wadanda Buhari ke son Majalisar ta amince da nadinsu akwai Umar Ibrahim El-Yakub daga Jihar Kano da kuma Goodluck Nnana Opia daga Jihar Imo.
Sauran su ne Ademola Adegoroye daga Jihar Ondo da Joseph Ukama daga Jihar Ebonyi da kuma Umana Okon Umana daga Jihar Akwa Ibom.
Akwai kuma Henry Ikechukwu Iko daga Jihar Abia sai kuma Odum Odi daga Jihar Ribas.