✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Buhari ya yi ta’aziyyar rasuwar Sarkin Sharifan Katsina

Buhari ya bayyana mamacin a matsayin wanda ya ke bawa gwamnatinsa gudummawa.

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya aike da sakon ta’aziyyarsa ga Masarautar Katsina kan rasuwar Sarkin Sharifai, Alhaji Abba Jaye.

Shugaban Kasar, ya sanar da hakan ne cikin wata sanarwa da hadiminsa kan kafafen watsa labarai, Garba Shehu, ya fitar, inda ya jajanta wa iyala da abokan arzikin mamacin.

Shugaba Buhari, ya ce marigayi Jaye na daga cikin wadanda suke taimaka wa gwamnatinsa ta hanyar ba da shawarwari da taimakon jama’a a yankinsa.

Buhari ya yi masa addu’ar samun rahama tare da fatan samun rabauta da aljanna.

Sannan ya ba wa iyalan mamacin hakuri kan wannan babban rashi.