Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya yi ta’aziyyar rasuwar Sarkin Sudan na Kontagora, Alhaji Saidu Umaru Namaska, wanda ya shafe shekara 47 yana mulki.
Shugaba Buhari ya yi wannan ta’aziyya ce a ranar Alhamis, inda ya bayyana Sarkin na Kontagora a matsayin wanda ya kawo nagarta da martaba ga sarautar gargajiya a cikin shekara 47 da ya yi a kan mulki.
- An rufe tashoshin motar bakin hanya a Katsina
- An rufe layin sadarwa a kananan hukumomi 13 na Katsina
Sakon ta’aziyyar na dauke ne a cikin wata sanarwa da Hadimin Shugaban Kasa kan Watsa Labarai, Garba Shehu, ya fitar, cewa Sarkin Sudan na Kontagora ya sadaukar da rayuwarsa wajen yi wa jama’arsa hidima.
Shugaban ya bayyana rasuwar sarkin a matsayin “wani babban rashi na daya daga cikin manyan masu rike da sarautun gargajiya a kasar nan.
“Hakika rasuwar Sarki Saidu Namaska babban rashi ne, bayan ya yi mulki na tsawon shekara 47, wanda hakan ya sa ya zama daya daga cikin sarakunan gargajiya mafiya dadewa a Najeriya.”
Shugaba Buhari ya mika ta’aziyyarsa ga gwamnatin Jihar Neja, Majalisar Sarakuna ta Jihar Neja da kuma iyalan mamacin.
Ya roki Allah da Ya ba wa marigayi Sarki Saidu Namaska maififciyar aljanna, sannan Ya saka masa da alheri game da ayyukansa.