✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Buhari ya yi ta’aziyyar rasuwar Muhammad Lele Mukhtar

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya jajanta wa iyalan tsohon Sakataren Gwamnatin Tarayya, Muhammad Lele Mukhtar, bisa rashinsa da suka yi. Buhari ya bayyana hakan ne…

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya jajanta wa iyalan tsohon Sakataren Gwamnatin Tarayya, Muhammad Lele Mukhtar, bisa rashinsa da suka yi.

Buhari ya bayyana hakan ne cikin wani jawabi da ya fitar ta hannun mai magana da yawunsa, Mallam Garba Shehu a ranar Talata.

Buhari ya mika sakon gaisuwar ga al’ummar jihar Bauchi, ‘yan uwa da kuma iyalan mamacin.

Buhari ya ce tsohon ‘Sarkin Dawakin Katagum’ din ya yi wa kasarsa hidima, cikin gaskiya da aminci.

Ya kara da cewa Alhaji Mukhtar mutum da ya ke da gaskiya da amana, kuma yana da hali na gari, wanda ya zama abun ko yi ga duk wanda ya zauna da shi.

A cewar Shugaban Kasar, mamacin ba ya ga kawo ci gaba a mahaifarsa ta Azare, ya kuma hidimtawa jihar Bauchi baki daya.

Sannan ya yi fatan Allah ya ba wa makusanta hakurin rashinsa, tare da rokon Allah ya masa rahama.