Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya bayyana farin cikinsa da sakin daliban Makarantar Sakandaren Kimiyya da ke Kankara da aka yi garkuwa da su a ranar Juma’ar da ta gabata, 11 ga watan Disambar 2020.
Buhari ya bayyana hakan ne a shafinsa na Twitter inda yake cewa: “Ina maraba da sakin daliban Makarantar Sakandiren Kimiyya ta Kankanra. Hakika sakin su zai kwantar da hankalin jama’ar kasar nan kwarai da gaske da ma duniya baki daya.
- Daliban Kankara na hanyar komawa gida —Gwamnatin Katsina
- Aisha Buhari ba ta ce komai kan Daliban Kanakara ba
“Al’umar kasar nan na cike da farin ciki bisa kwazo da namijin kokarin da Gwamnan Jihar Katsina, Aminu Masari, ya nuna tare da hukumomin tsaro da suka hada da sojoji da ’yan sanda da masu tara bayanan sirri,” inji Shugaba Buhari.
Idan ba a manta ba, a ranar Alhamis an saki wani bidiyo da ya yi ta yawo a shafukan sada zumunta, dauke da fuskokin yaran da kiraye-kirayen gwamnati ta samar da hanyar da za a samar da masalaha tsakanin kungiyar ba tare da amfani da karfin soji ba.
Daga baya a cikin dare Gwamnatin Jihar Katsina ta sanar cewa an sako daliban kuma kan hanyarsu ta zuwa gida bayan masu garkuwar sun sako su.
Shugaban Kwamitin Tsaro kuma Kuma Sakatare Gwamnatin Jihar, Mustapha Inuwa, ya ce a ranar Alhamis da dare ne Gwamnatin Jihar ta amso yara 340 daga hannun masu garkuwar a Tsafe, Jihar Zamfara mai makwabtaka da Jihar Katsina.
Gwamnatin jihar ta ce an ceto yaran ne bayan shiga tsakani da Shugaban Kungiyar Meyetti Allah na Kasa, Alhaji Muhammad Hardo Kiru ya yi.
Sun ce daliban da ke hanyarsu ta dawowa Jihar Katsina sun samu rakiyar masu shiga tsakani, jami’an tsaro domin dawo da su.
Wani bidiyo da ke yawo ya nuna yaran a cike da farin ciki a bayan wata babbar mota da dare a hanyarsu ta komawa Katsina.
Ana sa ran kawo su Gidan Gwamnatin Jihar su gana da Masari, yayin da aka yi masu masauki a sansanin alhazai inda ake sa ran Shugaba Buhari zai gan su kafin ya tashi zuwa Abuja bayan gama wani gajeren hutun da ya yi a gidansa da ke Daura.
Kishin-kishin din sako Daliban Kankara
Ranar Alhamis Gamayyar Kungiyoyin Arewa (CNG) ta janye zanga-zangar da ta shirya a Jihar Katsina ne naman a ceto daliban; ta ce ta janye ne saboda gamsuwa da bayanan da gwamantin ta yi mata cewa ta yi nisa a kokarinta na ganin masu garkuwar sun saki yaran.
Labarin sakin daliban na zuwa ne bayan ’yan sa’o’i da gwamnatin jihar ta karyata labarin sako su da Hadimar Shugaban Kasa, Abiki Dabiri-Erewa ta wallafa cewa an sako yara 333.
A ranar Alhamis din ce kuma kungiyar Boko Haram ta fitar da bidiyon da ta nuna yaran da ta ce daliban makarantar ne, domin tabbatar da cewa suna hannunta.
A ranar Juma’a da dare ne ’yan bindigar da suka musayar wuta da jami’an ‘yan sanda da ke tsaron makarantar suka yi awon gaba da daruruwan daliban.
Daga baya kungiyar Boko Haram ta yi ikirarin yin karkuwa da su, har ta fitar da bidiyon da wani daga cikin daliban ke neman gwamnatin Tarayya ta cece su, ta kuma biya bukatun kungiyar.
Gabanin haka Gwamnan Jihar Katsina, Aminu Masari, ya watsi da ikirarin da Boko Haram ta yi da farko cewa ita ce ta dauke yaran.
Bidiyon na biyu ya fito ne washegarin ran da Masari da Rundunar Tsaro ta Najeriya suka karyata ikirarin kungiyar na sace da daliban.
Kakakin Rundunar Tsaro, Manjo Janar, John Enenche ya ce ikirarin da na Boko Haram farfaganda ce kawai; kuma rundunar ta aiki don ceto daliban cikin aminci.
Shi kuma Masari cewa ya yi a iya saninsu masu garkuwa da mutane ne suka dauke yaran.
Jihar Katsina na daga cikin jihohin da suka fi fama da matsalar garkuwa da mutane a Najeriya.
Ya kara da cewa an gano yaran suna ajiye ne a ‘dajin Zamfara’, ana kuma tattaunawa da masu garkuwar kan sako daliban.