Shugaba Muhammadu Buhari ya bayyana harin da dan kunar-bakin-wake ya kai da safiyar ranar Talata a wani masallaci a garin Mubi na jihar Adamawa da aikin rashin imani kum abin kyama.
Furucin Buhari na kunshe ne a takardar sanarwar da Mai Taimaka Masa na Musamman kan Kafofin Yada Labarai da Wayar da Kan Jama’a, Malam Garba Shehu ya fitar a Abuja.
Shugaban ya yi ta’aziyya da iyalan wadanda lamarin ya rutsa da su da gwamnatin jihar da kuma daukacin mutanen jihar.