Shugaba Muhammadu Buhari ya yi ta’aziyyar mutuwar Moji Ladeji, yayar tsohon Gwamnan Jihar Ekiti, Ayodele Fayose.
Mai magana da yawun Shugaban Kasar, Femi Adesina ya wallafa ta’aziyar ta shafinsa na Facebook a ranar Laraba, 23 ga watan Satumba.
- Rasuwar Sarkin Biu rashi ne ga Najeriya – Buhari
- Buhari ya yi alhinin mutuwar Shugaban Jami’ar NOUN na farko
Shugaban Kasar ya kuma mika ta’aziyyarsa ga dukkanin abokai, makusanta da dangin marigayiya Moji dangane da wannan rashi da suka yi.
Ya nemi da su dauki dangana kasancewar mutuwa tana kan kowa.