Wata Babbar Kotun Tarayya da ke Akure, babban birnin Jihar Ondo, ta bayar da umarnin a ci-gaba da tsare wani zababben Sarki a jihar bisa zarginsa da gabatar da takardar shaidar karatu ta bogi.
Sarkin mai jiran gado na Araromi-Ekiti a Karamar Hukumar Ijero a Jihar Ekiti mai suna Yarima Babalola Adebomi ana zarginsa ne da yin amfani da takardun shaidar karatu na bogi guda biyu domin neman aiki a Asibitin Koyarwa na Jihar Ekiti.
- Yadda Mainin da Kiripto suka dauki hankalin matasa
- Kotun Duniya ta bai wa Isra’ila umarnin dakatar da kai hare-hare Gaza
Babban mai gabatar da kara na jihar Itunun Osobu ya shaida wa kotun cewa a shekarar 2008, wanda ake tuhuma Sarki mai jiran gado Yarima Babalola Adebomi mai shekara 48 ya yi amfani da satifiket din digiri na Jami’ar Ibadan da takardar kammala hidimar kasa (NYSC) na bogi domin samun gurbin aiki a Asibitin Koyarwa na Jihar Ekiti.
Itunun Osobu ya ce wanda ake tuhuma ya san cewa takardun biyu da ya yi amfani da su a wancan zamani na bogi ne kuma laifi ne da ya saba wa sassa na 1(2) (c) da 12 na kundin manyan laifuffuka.
Lauyan da kariya, Barista Attah Paul ya roki kotun ta bayar da belin wanda ake tuhuma saboda wasu dalilai masu karfi musamman a cewarsa Yarima Babalola Adebomi ba zai tsere ba domin ya mallaki kadarori a jihar.
Sai dai alkalin kotun Mai shari’a Owoeye ya yi watsi da rokon kuma ya bayar da umarnin a ci-gaba da tsare zababben Sarkin a ofishin Mataimakin Sufeto Janar na ’Yan sanda har zuwa ranar 23 ga watan Mayu inda za a ci gaba da sauraron karar.