Kungiyar Makiyaya ta Miyetti Allah a Kudu maso Yamma ta yi maraba da kafa kwamitin shiga tsakanin manoma da makiyaya da Gwamnatin Jihar Ekiti ta yi don samar da zaman lafiya da wadataccen abinci a kananan hukumomi 16 na jihar.
Da yake kaddamar da kwamitin a madadin Gwamnan Jihar Biodun Oyebanji, Kwamishinan Ayyukan Gona, Mista Ebenezer Boluwade ya ce, gwamnati ta amince da kafa kwamitin ne don kawo ƙarshen rikicin manoma da makiyaya da kuma samar da zama lafiya da wadataccen abinci a jihar.
- Sojoji sun ceto mata da yara 57 a Dajin Sambisa
- An canja masa halitta zuwa mace ba tare da izininsa ba
Ya ce Majalisar Sarakunan Gargajiya da Rundunar ’Yan sanda da Kungiyar Manoma Ta Kasa (AFAN) da Kungiyar Miyetti Allah a jihar suna cikin wakilan wannan kwamiti wanda shi ne irinsa na farko da wata gwamnati ta kafa a Kudancin kasar nan.
A hira da Aminiya bayan kaddamar da kwamitin a Ado-Ekiti babban birnin jihar, shugabannin kungiyar sun nemi gwamnatocin jihohin Arewa su yi koyi da Gwamnatin Jihar Ekiti wajen kafa irin wannan kwamiti a jihohinsu don kawo ƙarshen rikicin manoma da makiyaya da ya ki ci, ya ki cinyewa a Nijeriya.
Da yake yi wa Aminiya ƙarin haske kan ayyukan kwamitin Shugaban Ƙungiyar Miyetti Allah ta Jihar Ekiti, Alhaji Muhammadu Nasamu ya ce kwamiti yanzu shi ne ke da wuƙa da nama wajen sauraron korafe-korafen Fulani da makiyaya a jihar.
“Daga yanzu wannan kwamiti ne zai riƙa sauraron dukkan koke-koke na sabanin da aka samu a tsakanin manoma da makiyaya ba tare da ’yan sanda sun shiga cikin lamarin ba.
“Kuma kwamitin ba zai amince da ƙarin kuɗi da manoma suke yi a kan amfanin gona da dabbobi suka lalata ba.
“Su kuma makiyaya za a tabbatar da cewa sun nuna hakuri wajen amincewa da duk asarar da suka yi,” in ji shi.
Alhaji Muhammadu Nasamu ya jinjina wa gwamnatin Ekiti kan kafa kwamitin don samar da zaman lafiya a tsakanin manoma da makiyaya a jihar.
Sai ya nuna matuƙar baƙin ciki a kan gazawar gwamnatocin jihohin Arewa kan gaza shawo kan irin wannan matsala a jihohinsu.
Ya ce maimakon haka sai kara ruruta wutar fitina suke yi ta hanyar kafa kungiyoyin ’yan banga.
“Tuntuni muka hango cewa muddin ana so a yi maganin rikicin manoma da makiyaya a Arewa wajibi ne gwamnatocin Arewa su janye ayyukan ’yan banga a jihohinsu,” in ji shi.
Shugaban Kungiyar Miyetti Allah reshen Jihar Ondo da ke makwabtaka da Ekiti, Alhaji Bello Garba ya ce, ana zaton wuta a makera ce sai aka same ta a masaka a lamarin baki dayansa.
“Kamata ya yi a ce jihohin Kudu suna yin koyi da Arewa wajen lalubo hanyar magance rikicin manoma da makiyaya, amma abin takaici yanzu muna kira ne ga gwamnatocin Arewa su yi koyi da Gwamnatin Jihar Ekiti.
“Domin mu a Jihar Ondo gwamnati ta kammala dukkan shirye-shiryen kaddamar da irin wannan kwamiti.
“Mun zauna a teburi daya da dukkan masu ruwa-da-tsaki inda muka bayar da shawarwari aka mika su ga Gwamna domin neman amincewa da sa hannunsa a kafa kwamitin shiga tsakanin manoma da makiyaya a Jihar Ondo,” in ji shi.
Aminiya ta gano cewa mahalarta taron na Jihar Ekiti sun hada da sarakuna da shugabannin ƙungiyoyin manoma da makiyaya daga ƙananan hukumomi 16 na jihar da wakilin Hedikwatar Ƙungiyar Miyetti Allah daga Abuja.