Shugaban Kasa Muhammadu Buhari, ya yi alhinin mutuwar Sanata Yusha’u Muhammad Anka, wanda ya koma ga Mahaliccinsa a ranar Litinin kuma aka binne shi ranar talata a birnin Abuja.
Buhari cikin sanarwar mai magana da yawunsa, Mallam Garba Shehu ya fitar a ranar Talata, ya bayyana mamacin a matsayin dan gwagwarmayar goyon bayan gaskiya kuma mai tsananin adawa da duk wani lamari da yake ganin ya kauce wa hanyar daidai.
Sanarwar ta ce “Sanata Anka mutum ne mai kishin kasa wanda adalci da riko da gaskiya shi ne tafarkin da ya rika kuma hakan ya sanya ya samu girmamawa da dukkan bangarorin al’umma da na siyasa.”
“Ina rokon Allah ya jikansa da rahama ya kuma kyautata makwancinsa.”
Marigayin Sanatan shi ne wanda ya wakilci Shiyyar Zamfara ta Yamma a zauren Majalisar Dattawa daga watan Mayun shekarar 1999 zuwa Mayun 2007, inda ya tsaya tsayin-daka wajen ganin neman wa’adin mulki na uku bai tabbata ba wanda aka nemi kawo wa kasar a shekarar 2006.