✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Buhari ya ware N21.9bn domin gina asibitin duba lafiyarsa

Asibitin zai rika duba lafiyar shugabannin kasashen Afirka.

Shugaba Muhammadu Buhari ya amince a gina karamin asibiti mai gado 14 a kan Naira biliyan 21.9 domin duba lafiyar shugaban kasa a Asibitin Fadar Shugaban Kasa.

Babban Sakataren Fadar Shugaban Kasa, Umar Tijjani, ya ce bangaren zai kuma rika duba lafiyar shugabannin kasashen Afirka, kuma za a fara aikin ne a ranar Litinin, wanda aka ba wa kamfanin Julius Berger kwangilar.

Da yake kare kasafin kudin Fadar Shugaban Kasa na 2022 a gaban Majalisar Dattawa, Umar Tijjani bangaren duba lafiyar shugaban kasan yana da lambu, dakunan tiyata, dakin gwaje-gwaje, wurin daukar hoto, da dakin shan magunguna.

“Bene ne mai hawa daya da kuma ginin karkashin kasa, kuma yana da dakin dakunan tiyata, da daki kwana na alfarma na musamman, dakin killacewa na alfarma da kuma wasu dakunan killacewa guda shida,” inji shi.

Ya bayyana cewa, “Gwamantin da ta gabata ce ta kirkiro aikin a 2012 a kan Naira biliyan 21 kuma yana da gadon kwantar da marasa lafiya 14”.

A cewarsa, za a kammala gina asibitin ne a watan Disamban 2022, kuma “Yawancin ayyukan sharan fagen an kammala su, Shugaban Kasa ya amince a yi aikin, hakazalika Hukumar Kula da Sayen Kayyakin Gwamnati.”

Kwamitin Majalisar Dattawan, karkashin Sanata Danjuma La’ah, ya yaba da yunkurin, tare da cewa zai kai ziyarar gani da ido a cikin watan Disamban 2021.