Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya aike da tawagar jami’an tsaro ta musamman zuwa jihohin Sakkwato da Katsina don dakile ayyukan ’yan bindiga a jihohin.
Mai magana da yawun shugaban kasa, Malam Garba Shehu ne, ya sanar da hakan a ranar Juma’a.
- Karin kudin mai: Za mu maka gwamnati a kotu —Jama’ar Funtua
- Sudan: An kashe mutum 138 a sabon rikicin kabilanci a Darfur
Garba Shehu, ya ce Buhari na jiran rahoto cikin gaggawa da kuma shawarwari kan matakin da ya kamata a dauka domin magance matsalolin da jihohin ke fuskanta.
Tawagar da Buhari ya tura ta hada da mai ba shi shawara kan harkokin tsaro, Manjo Janar Babagana Monguno mai ritaya da Shugaban Sashen Kwararru na Tsaron Kasa, Manjo-Janar Samuel Adebayo da kuma Babban Sufeton ’Yan Sandan Najeriya, Usman Alkali Baba.
Sauran sun hada da Darakta-Janar na Hukumar Tsaro ta Farin Kaya, Yusuf Magaji Bichi, da Darakta-Janar na Hukumar Tattara Bayanan Sirri ta Najeriya Ambasada Ahmed Rufa’i Abubakar.
Wannan matakin dai na zuwa ne bayan mutane daga yankin Arewacin Najeriya sun nuna bacin ransu kan kasshe-kashen da ake musu tare da garkuwa da mutane a yankin.
Matsaltar ta fusata mutane har suka fito suka gudanar da zanga-zangar neman Shugaba Buhari ya sauka daga mulki a ranar Juma’a, kan abin da suka kira da gazawarsa.