✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Buhari ya tura babban hafsan sojin sama zuwa Zamfara

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya umurci babban hafsan sojin sama Air Marshall Abubakar Baba Sadiq ya kai ziyara Zamfara da Sakkwato a yau da gobe…

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya umurci babban hafsan sojin sama Air Marshall Abubakar Baba Sadiq ya kai ziyara Zamfara da Sakkwato a yau da gobe don dakile matsalar ‘yan bindiga da ‘yan fashi da makami da kuma masu garkuwa da mutane da ake fama da ita jihohin.

Wata sanarwar da kakakin Shugaban na Najeriya Malam Garba Shehu ya fitar, Buhari ya ce, hafsan sojin zai yi hutun Kirsimetinsa a jihohin biyu kuma dole ne a kawo karshen kashe-kashen da ake yi a jihohin.

Shugaba Buhari ya yi Allah wadai da kashe-kashen mutane da aka yi a kananan hukumomin Birnin Magaji da Tsafe da Maradun da wasu yankuna na jihar Zamfara, wanda ake zargin ‘yan fashi da aikata wa.