✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Buhari ya tsawaita aikin kwamitin COVID-19

Ya sake kara wa'adin kwamitin tare da rokon a hada kai wurin fadakar da jama’a

Shugaba Muhammadu Buhari ya kara tsawaita wa’adin aikin kwamitin da ya kafa kan yaki da cutar COVID-19 zuwa watan Maris na 2021.

Buhari ya ce hikimar yin hakan shi ne domin a dora a kan nasarorin da aka samu a wata tara da aka dauka ana yaki da cutar wadda ta sake dawowa.

“Na tsawaita wa’adin aikin Kwamitin Shugaban Kasa (PTF) kan Yaki da COVID-19 zuwa karshen watan Maris, 2021, duba da sake bazuwar cutar da kuma yunkurin samun rigakafi.”

Ya kara da kira ga masu ruwa da tsaki su kara zage damtse da kuma yin aiki tare wurin yakar cutar da ta sake dawowa kuma kuma barazara a Najeriya.

“Ina rokon gwamnatocin jihohi, sarakuna, shugabannin addini da na al’umma da su hada kai da PTF wurin fadakar da jama’a a dukkannin matakai,” inji shi.

Shugaba Buhari ya yi jawabin ne bayan ganawar da ya yi da kwamitin, wanda ya gabatar masa da rahoton aikinsa na karshen shekara a ranar Talata.